Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin Tarayya
Published: 14th, June 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya.
Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya.
“Mu a matsayimmu na ƙasa mai son zaman lafiya, muna roƙon ƙasashen da ke rikici da su zauna su tattauna maimakon su ci gaba da faɗa.”
Gwamnatin Tarayya ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya, musamman Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da su ɗauki matakai don hana yaɗuwar rikicin da kuma samo hanyar warware matsalar.
Sanarwar ta ƙara da cewa amfani da ƙarfin soji ba shi da amfani matuƙa, domin faɗa ba zai kawo sauƙi ba.
Najeriya ta ce a shirye ta ke ta bayar da taimako domin hana yaɗuwar rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Iran Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Iran tana da hakkin mayar da martani ga Isra’ila : Sanarwar Ma’aikatar harkokin waje
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ce mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila hakki ne na shari’a ga Iran kamar yadda doka ta 51 ta kundin tsarin mulkin MDD ta tanada.
Da farko dai ma’aikatar ta mika ta’aziyyar shahadar wasu kwamandoji da jami’an kasar Iran a harin da Isra’ila ta kai wa kasar.
“Hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa Iran sun sabawa doka ta 4 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya a matsayin wani mataki na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma Iran tana da hakki na shari’a na halal ta mayar da martani kan wannan zalunci kamar yadda yake a cikin sashe na 51 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya.
Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare al’ummar Iran da dukkan karfinsu.”
“Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mamba a Majalisar Dinkin Duniya, tana mai jaddada wajibcin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na daukar matakin da ya dace wajen tunkarar matsalar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, sakamakon wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan take yi wa Iran.
“Dukkan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya, musamman na shiyya da na Musulunci, da ‘yan gwagwarmaya, da dukkan duniya ana sa ran nan take za su yi Allah-wadai da wannan aika-aika da kuma daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa don tinkarar wannan kasada mai hatsarin gaske wadda ko shakka babu ta nuna yadda zaman lafiya da tsaro a duniya ke cikin wata babbar barazana da ba a taba ganin irinsa ba.”
Iran, ta kuma babu shakka wannan danyen aikin da Isra’ila ta aikata ya samu sahalewar Amurka, don haka a cewar Tehran, Amurka na da hannu a wannan hare haren na Isra’ila.