HausaTv:
2025-07-29@12:56:40 GMT

Jagora: “Yan Sahayoniya Su Saurari Ukuba Mai Tsanani

Published: 13th, June 2025 GMT

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fitar da bayani a yau juma’a da a ciki ya yi wa ‘yan sahayoniya alkawalin fuskantar ukuba mai tsanani.

Bayanin na jagora ya kunshi cewa:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ya Ku Al’ummar Iran Masu Girma

Da safiyar yau, ‘yan sahayoniya sun miko hannuwansu da suke jike da jini, domin tafka laifuka a cikin kasarmu.

 Sun kuma sake bayyana hakikanin dabi’arsu mummuna fiye da kowane lokaci a baya,  su ka kai wa  gidajen fararen hula hari. A dalilin haka, wannan haramtacciyar kasar ta saurari sakamako mai tsanani.

Su kuma  sani cewa; Sojojin Jamhuriyar musulunci masu karfi ba za su kyale su ba da yardar Allah. A yayin wannan harin kwamandoji da dama da masana sun yi shahada.

Wannan laifin da ‘yan sahayoniya su ka tafka, ya sa sun shirya wa kansu makoma mai tsanani da daci, za su kuma ga hakan babu tantanma.

Sayyid Ali Khamnei

13/06/2025

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Iran Da Rasha                                                                                                                       

Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran.

Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba.

A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da wadannan tsare-tsare.”

Ya kara da cewa, manufar farko ita ce raunana gwagwarmaya da yanke  alakar Iran da yankin Caucasus da kuma killace Iran da Rasha ta kasa a kudancin yankin.

Ya bayyana cewa: “Wannan aikin ba wai kawai wani bangare ne na shirin Amurka na maye gurbin Ukraine da yankin Caucasus a matsayin wani sabon fage na matsin lamba kan Rasha da Iran ba, amma ana aiwatar da shi ne tare da goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO da kuma wasu kungiyoyin ‘yan kishin kasa na Turkiyya (Pan-Turkist).

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  • Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba
  • Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
  • Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Iran Da Rasha                                                                                                                       
  • An Yanke Hukuncin Kisa Kan Yan MKO A Nan Iran
  • Iran Da Afganistan Sun Tattauna Dangane Da Komawar Afganawa Gida
  • Sojojin HKI Sun Kutsa cikin Jirgin Ruwan “Hanzala” Dake Son Karya Killace Yankin Gaza
  • Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kiran Cewa; Ina Masu Fafatukar Kare Hakkin Dan Adam Suke A Bala’in Gaza?
  • Jagora: Za’a Gaggauta Ci Gaba A Ilmi Da Fasahar Tsaron Sojojin Kasar