Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci
Published: 14th, June 2025 GMT
Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta tarayya ta sanar da gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku domin neman taimakon Allah wajen kare ƙasar nan da kuma tabbatar da wadatar abinci. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da aka fitar a ranar 11 ga Yuni, 2025, wadda Daraktar Gudanarwa, Mrs. Adedayo Modupe O.
, ta sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, dukkanin daraktoci, da mataimakan daraktoci, da shugabannin sassan sarrafa kayayyakin amfanin gona da sauran ma’aikatan ma’aikatar za su halarta. An sanya wa wannan shiri suna “Neman Taimakon Ubangiji Don Kariya da Cigaban Kasa.”
Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban Zangon Noma Da Kiwo Ɗauke Da Kasuwar Duniya A JiharModupe ta bayyana cewa manufar wannan addu’a ita ce neman jagorancin Allah da tallafinsa ga ƙoƙarin gwamnati wajen samar da ingantaccen tsarin abinci mai ɗorewar a fadin ƙasa. Za a gudanar da zaman addu’ar ne a shalƙwatar ma’aikatar da ke Abuja a ranakun Litinin: 16, 23 da 30 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta buƙaci dukkan ma’aikata su kasance cikin azumi domin samun tsarkakewa da shiri na musamman wajen roƙon Allah game da matsalolin da ke addabar fannin noma da tsaron abinci a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Bakai’i: Iran Tana Son Ganin An Yi Taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa;Yunwar da mutanen Gaza suke fama da ita na tsawon watanni biyar, laifi ne maras tamka da HKI take tafkawa, da ya zama wajibi kungiyar kasashen musulmi ta yi taron gaggawa akansa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Dr. Isma’ila Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya kuma yi Magana akan tattaunawar da Iran ta yi da kasashen turai akan shirinta na makamin Nukiliya, ya ce: Tattaunawar da aka yi ta da kasashen turai manufarta ita ce dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata akan shirinta na Nukiliya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Kasashen na turai ba su da hakkin su kakabawa Iran takunkumi, idan kuwa har su ka ci gaba to za su fuskanci mayar da martanin Iran.