HKI Ta Rufe Filin Saukar Jiragen Sama Na Ben Gorion Tare Da Dauke Jiragenta Zuwa Waje
Published: 14th, June 2025 GMT
Mai magana da yawun hukumar da take kula da filin saukar jiragen sama ta Ben Gorion ta sanar a yau Asabar cewa an rufe filin saukar jiragen saman har zuwa wani lokaci a nan gaba, bayan da aka dauke dukkanin jiragen sama zuwa kasashen Cyprus, Greece da kuma Amurka.
Mai Magana da yawun hukumar filin saukar jiragen saman na Ben Gorion Lisa Daiper ta bayyana ce; Babu wani lokaci takamaimai da aka tsayar domin sake bude filin saukar jiragen saman na Ben Gorion.
A gefe daya jaridar “Maariv’ ta bayyana cewa; An dauke dukkanin jiragen sama zuwa filayen jiragen saman a kasashen turai.
Haka nan kuma ta kara da cewa; An dauki 14 daga cikin jiragen saman na HKI zuwa filin saukar jiragen saman a Laranka da Papus dake tsibirin Cyprus da su ne filayen jiragen sama na nahiyar turai mafi kusa da HKI.
Su kuwa jiragen da shugabannin ‘yan sahayoniya suke shiga an kai su ne zuwa filin jirgin sana na birnin Athenia na kasar Girka, wasu kuwa zuwa kasashen Bulgari da Faransa.
Dauke jiragen na ‘yan sahayoniya dai ya zo ne saboda tsoron kar makamai masu linzami na Iran su isa gare su.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: filin saukar jiragen saman filin saukar jiragen sama
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Gummi yana wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara a majalisar wakilai.
An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkukuMai shari’a Obiora Egwuatu ne, ya yanke hukuncin, inda ya umarci kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da ya daina amincewa da Gummi a matsayin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum.
Haka kuma ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta shirya sabon zabe cikin kwanaki 30 domin cike gurbin kujerar dan majalisar.
Jam’iyyar PDP tare da shugaban ta na jihar Zamfara, Jamilu Jibomagayaki, ne suka shigar da karar dan majalisar.
Sun ce bai dace Gummi ya ci gaba da zama a kujerar ba bayan barin jam’iyyar da ta tsayar da shi takara.
Gummi, ta bakin lauyansa ya ce ya fice daga PDP ne saboda rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi a matakin kasa da kuma a mazabarsa.
Amma kotu ta yi watsi da wannan hujjar, inda ta bayyana cewa babu takaddama da za ta ba shi damar ya sauya sheka.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Egwuatu ya ce ’yan siyasa dole su mutunta zabin jama’ar da suka kada musu kuri’a a karkashin jam’iyyar da ta tsayar da su takara.
Ya ce doka ba ta yadda da dan siyasa ya bar jam’iyyar da ta taimaka masa wajen lashe zabe sannan ya koma wata jam’iyya ba tare da ajiye mukaminsa ba.
Ya kara da cewa kuri’un da aka kada don dan takarar na jam’iyya ne, ba nasa ne na kashin kansa ba.
“Idan mutum yana son sauya sheka, ka da ya dauki amanar jama’ar da ta zabe shi ya tafi da ita,” in ji alkalin.
Kotu ta kuma umarci Gummi da ya daina karbar albashi da wasu hakkoki a matsayin dan majalisa, tare da mayar da duk kudaden da ya karba daga ranar 30 ga watan Oktoba, 2024, zuwa ranar da aka yanke hukuncin.
Haka kuma, ya gabatar da hujjar mayar da kudaden ga kotu cikin kwanaki 30.
Mai shari’a Egwuatu ya kuma ci Gummi tarar Naira N500,000, domin biyan PDP kudaden da ta kashe wajen shigar da kara.