HausaTv:
2025-10-13@17:49:56 GMT

Masana Ilimin Nukiliyar Iran Sun Yi Shahada

Published: 13th, June 2025 GMT

A sandiyyar harin da ‘yan sahayoniya su ka kawo wa Iran da asubahin yau, masana fasaahr Nukiliya da dama sun yi shahada.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambaci cewa: Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran; Faridun Abbasi. Shugaban jami’ar Azad, Muhammad Mahdi Dahranji.

Shugaban Kwalejin fasahar Nukiliya, Abdulhamid Minochehri. Hakan nan kuma Malamin fasahar Nukiliya Ahmda Riza Zulfiqar, sai mataimakin shugaban hukumar  makamashin Nukiliya Amir Husain Fiqhi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa.

Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu.

’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno

Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a.

Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai.

Jami’an hukumar daga sashen Doguwa sun tare su a ƙofar Riruwai da ke Doguwa yayin da suke ɗauke da manyan jakunkuna uku cike da tabar wiwi.

Babban wanda ake zargi shi ne Yusuf Alasan, mai shekara 25, tare da abokan aikinsa biyu; Muktar Musa da Musa Sani.

Kwamandan, ya ce hukumar ta kammala binciken farko kuma ta miƙa su tare da kayan da aka kama zuwa ofishin NDLEA na Jihar Kano don yin ƙarin bincike.

Bodinga, ya ƙara da cewa NSCDC za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da laifuka da tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
  • Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh
  • Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk
  • ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
  • Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho
  • Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano