An rufe taron ministocin Sin da Afirka mai tabbatar da ci gaban hadin gwiwar da aka samu a dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka gudanar daga ranekun 10 zuwa 12 a birnin Changsha na lardin Hunan, matakin da ya bayar da sabbin damammaki ga kasashen Afirka, bisa shirin “manyan ayyuka 10 na abota tsakanin Sin da Afirka”.

Sa’an nan, bayan an kammala taron, nan take, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyaki hajojin Sin da Afirka karo na 4, duk a birnin Changsha, matakin da ya zamo daya daga cikin jerin ayyukan da ake gudanar da su don aiwatar da shirin “manyan ayyuka 10”, inda aka baje kolin ci gaban da aka samu, da tattara damammaki da albarkatu wuri guda, domin gaggauta samun ingantacciyar bunkasar hadin gwiwar Sin da Afrika a bangaren ciniki da tattalin arziki.

A cikin shekaru 25 da suka gabata, tun kafuwar FOCAC a shekarar 2000, yawan kudin kayayyakin da ake shigarwa da na fitarwa tsakanin Sin da Afirka ya karu zuwa dalar Amurka biliyan 292.4 a shekarar 2024 daga dalar biliyan 13.9 a 2000, inda adadin ya karu da fiye da ninki 20. Kana a cikin wasikar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika don taya murnar cimma nasarar gudanar da taron ministoci na wannan karo, Xi ya sanar da shirin yafe harajin kwastam na kaso 100% a kan kayayyakin kasashen Afirka 53, wadanda suka kulla dangantakar diflomasiyya da Sin, matakin da zai kara saukaka wa kasashen Afirka a fannin fitar da kayayyakinsu zuwa kasar Sin.

Kazalika, a farkon watanni 5 na bana, yawan kudin da Sin ta kashe wajen shigo da kayayyakin Afrika zuwa cikin kasarta ya kai dalar Amurka biliyan 50.6, adadin da ya karu da kashi 1.6% bisa na makamancin lokacin bara. Hakan ya ba kasashen Afirka damar more babbar kasuwar Sin.

Hadin gwiwar Sin da Afirka na kara habaka, duba da yadda ake aiwatar da hakikanan matakai don tabbatar da manyan tsare-tsare da aka cimma, tare da mai da hankali matuka kan amfanar da al’ummun Afirka, da inganta karfin kasashen Afirka na samun bunkasuwa bisa dogaro da kai. Ma iya cewa, hadin gwiwar bangarorin Afirka da Sin ta fuskar ciniki da tattalin arizki na cikin wani yanayi mai armashi da dorewa, duk da kalubaloli, da sauye-sauyen yanayin da ake fuskanta a duniya, abin da sa ake samun cikakken kwarin gwiwa bisa hadin gwiwar kasashe masu tasowa da bunkasar duniya baki daya. (Mai zane da rubutu:MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hadin gwiwar

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.

Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.

Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Ya ce an tsara wannan asusu  ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.

Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.

Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin  ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.

Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a  wuraren.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15
  • Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai