Bin Hanya Daya Da Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Muhimmin Mataki Ne Na Ba Da Tabbaci Ga Huldar Ciniki Da Tattalin Arzikin Sin Da Amurka
Published: 13th, June 2025 GMT
Kafofin yada labarai na kasa da kasa na matukar zura ido kan taron farko na tsarin tattaunawa game da tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka da aka gudanar tsakanin ranekun 9 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki a London na kasar Burtaniya.
An yi muhimmin shawarwarin ne kan matsaya daya bisa manyan tsare-tsaren da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ran 5 ga watan nan.
Ban da wannan kuma, kasashen biyu sun samu sabon ci gaba kan batutuwan ciniki da tattalin arziki da suka tasa a gaba. Kazalika, bangarorin biyu sun nace ga bin hanya iri daya da tabbatar da matsaya daya da suka cimma.
A ganin wani farfesa na kwalejin koyar da ilmin diflomasiyya ta kasar Sin Li Haidong, tsarin tattaunawa da kasashen biyu suka cimma na bayyana niyyarsu ta tabbatar da huldarsu yadda ya kamata, kuma zai daidaita bambancin ra’ayinsu a sabon mataki da ma warware batutuwan ciniki da tattalin arziki da suka tasa a gaba, kana da ingiza bunkasa huldarsu a wannan bangare cikin kwanciyar hankali. A sa’i daya kuma, ci gaban da suka samu na biyan bukatun al’ummun duniya, tare da bayar da ingantaccen karfin raya tattalin arzikin duniya baki daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da tattalin arziki da
এছাড়াও পড়ুন:
Bakai’i: Iran Tana Son Ganin An Yi Taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa;Yunwar da mutanen Gaza suke fama da ita na tsawon watanni biyar, laifi ne maras tamka da HKI take tafkawa, da ya zama wajibi kungiyar kasashen musulmi ta yi taron gaggawa akansa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Dr. Isma’ila Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya kuma yi Magana akan tattaunawar da Iran ta yi da kasashen turai akan shirinta na makamin Nukiliya, ya ce: Tattaunawar da aka yi ta da kasashen turai manufarta ita ce dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata akan shirinta na Nukiliya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Kasashen na turai ba su da hakkin su kakabawa Iran takunkumi, idan kuwa har su ka ci gaba to za su fuskanci mayar da martanin Iran.