Yayin taron shekara-shekara na tattaunawar CBD na shekarar 2025 da aka rufe a yau Juma’a 13 ga wata, mashawarci kana kwararre a hukumar kasuwancin kasar Sin ta kasar Birtaniya, kuma shugaban cibiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Birtaniya da Sin mista John Mclean, ya bayyana yayin da yake hira da wakilin CMG cewa, kasuwar kasar Sin tana cike da damammaki, don haka dole ne ya shiga a dama da shi a cikinta.

A ganinsa, yayin da ake tinkarar tashe-tashen hankula da rashin tabbaci a duniya, babbar baiwar da Sin take da ita, da muhalli mai aminci da bude kofa ga kowa, sun samarwa kamfanonin Birtaniya da ma duniya baki daya damammaki.

Tun bayan kafuwarsa a shekarar 2000 zuwa yanzu, taron ya kasance dandali da kasar Sin ke tattaunawa da kasashen duniya. A yayin taron bana, wakilai fiye da 6000 daga sassan siyasa, da kasuwanci, da ilimi da suka fito daga kasashe da yankuna fiye da 40 sun halarta. A lokacin gudanar da taron, wasu mahalartansa sun yi nuni da cewa, kasar Sin na da babbar juriya wajen raya tattalin arziki, da kuma babbar baiwar raya kasa. Haka kuma, gwamnatin Sin ta gaggauta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, lamarin da ya zuba sabon kuzari ga kamfanonin kasashen waje, ta yadda suke shiga a dama da su wajen yin ciniki a kasar Sin.

A yayin bikin bude taron, mahalartansa sun yi kira da a gina duniya mai tsabta, da kyawu, da dorewa cikin hadin gwiwa, duba da ganin kasar Sin ta ba da babbar gudummawa, ta kuma yi iyakacin kokari a fannin raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma rage fitar da sinadarin carbon. Alkaluma sun nuna cewa, yanzu haka kasar Sin tana daya daga cikin kasashen da suka fi saurin rage yawan makamashi mai dumama yanayi da suke amfani da shi da samun kyautatuwar iska, ta kuma dasa yawan bishiyoyi, da ciyayi da fadinsu ya kai rubu’i bisa jimillar fadin sabbin bishiyoyi da ciyayi na duniya baki daya, tare da kafa tsarin makamashin da ake sake amfani da shi mafi girma, kuma mafi saurin ci gaba a duniya, baya ga kafa tsarin masana’antu na sabbin makamashi mafi girma kuma cikakke a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Sin ta

এছাড়াও পড়ুন:

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Yola

Ruwan sama mai ƙarfn gaske ya haddasa mummunar ambaliya a Yola ta Kudu, Jihar Adamawa, inda mutane da dama suka mutu, yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu.

Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Shagari, Sabon Pegi da Anguwan Tabo.

Ayyukan ceto suna ci gaba da gudana, inda Sojoji da hukumomin agaji ke kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa.

Hukumomi sun shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su gaggauta barin wuraren, kasancewar ana hasashen karin ruwan sama.

 

RN

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin
  •  Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta
  • An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
  • Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Yola
  • Amurka Ta Dakatar Da Bai Wa ‘Yan Kasar Nijar Bisa Shiga Cikin Kasarta
  • Taron ‘Kasashe biyu’ A Gefen Taron MDD A NewYork
  • Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5
  • Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kiran Cewa; Ina Masu Fafatukar Kare Hakkin Dan Adam Suke A Bala’in Gaza?
  • Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Falasdinu A Birnin Tunis Fadar Mulkin Kasar Tunusiya