Rawar Da ‘Yan Wasan Afirka Suka Taka A Gasar Premier Ta Ingila
Published: 15th, June 2025 GMT
Semenyo ma ya taka rawar gani saboda kwallo biyun da ya ci a wasan karshe sun sa ya ci wa kungiyarsa Bournemouth kwallo 11 kenan a karonfarko.
Danwasan Najeriya Aled Iwobi ya fi abokan wasansa kokari a Fulham da kwallayensa tara da ya ci da kuma taimakawa wajen cin shida, sannan ya dan dara Amad Diallo na Manchester United (wanda ya ci takwas kuma ya bayar aka ci shida).
Thomas Partey na Ghana ya fi yawan tura cikakkun fasin (1,631). Shi kuwa Idrissa Gana Gueye ya nuna bajintarsa ne wajen taimka wa Eberton samun damar ci gaba da zama a gasar. Dan Senegal din mai shekara 35 ya cim ma mafi girman bajintar dakatar da abokan hamayya sau 133 kuma ya dauke kwallo daga abokin hamayya sau 221, inda ya zarta kowane dan kwallo daga nahiyar Afrka.
Aaron Wan-Bissaka, shi ne ya fi kowa tare kwallo (66) kuma ya fi yawan yin yanka (64) a ‘yanwasan bayan Premier League – hakan ya sa magoya bayan West Ham suka zabe shi gwarzonsu a bana. Dan Ajeriya Rayan Ait-Nouri, wanda ya koma kungiyar Manchester City a wannan watan ya nuna bajintar kai hari duk da matsayinsa na danwasan baya ta gefe, inda ya ci wa tsohuwar kungiyarsa ta Wolbes kwallo hudu kuma ya bayar aka ci bakwai.
Dan wasa Ola Aina ya taka rawa mafi kyau a tarihi sana’arsa a Nothingham Fores, inda ya dinga kwalo daga ƙafar abokan hamayya sau 190 – mafi yawa kenan da wani danwasan baya ya taba yi. Dan Najeriyar mai buga baya a bangaren dama ya cire kwallo daga kan layin shiga raga sau uku, wanda ‘yanwasa shida ne kawai suka iya yin irin wannan bajintar cikinsu kuma har da Iliman Ndiaye na Senegal.
Calbin Bassey na Najeriya ya taba kwallo sau 2,536 a Fulham – fiye da kowane dankwallon Afirka kenan a gasar – da cikakken fasin 1,926 da ya bayar, da tsige kwallo sau 113, da hana kwallo wucewa sau 17. A gefe guda kuma, Noussair Mazraoui ya tare abokan hamayya sau 115 da kuma dauke kwallo sau 216 daga abokin hamayya a Manchester United.
Andre Onana, mai tsaron raga dan Afirka tilo a Premier League, ya fuskanci kalubale mai girma a kakar bana yayin da Manchester United ta shiga tasku mafi muni cikin shekara 50. Mai tsaron ragar na Kamaru ya buga wasa tara ba tare da an zira masa kwallo a raga ba, amma kuma an ci shi kwallo 44 cikin wasa 25. Hana kwallo shiga raga sau 90 da ya yi shi ne karo na 12 kuma mafiya yawa,
inda adadin ya zama kashi 66 cikin 100 kuma na 15 kenan a tsakanin masu tsaron da suka buga wasa 10 ko fiye da haka. Danwasan mai shekara 29 ya yi kuskure uku da suka jawo zira masa kwallo a raga – ‘yanwasa uku ne kawai suka yi fiye da hakan.
Tarihi mara amfani
Danwasan da ya fi kowa yin keta a kakar Premier ta 2024-25 shi ne, Semenyo na Bournemouth, wanda aka busa wa laifi sau 73. Adadin ya zarta na kowane dan wasan Afirka. Samy Morsy na Ipswich Town da kasar Masar, shi ne ya fi kowanne dan Afirka samun katin gargadi (10), sai Gueye da Semenyo da ke da 9 kowanne. An kwace kwallo daga kafar Mohammed Kudus na Ghana da West Ham sau 93, sannan ya buga kwallon da ta daki turke sau shida. Salah da Jackson da Palmer ne kawai suka zarta shi.
Danwasan gaban Chelsea da Senegal Jackson ya yi satar gida fiye da kowa har sau 23. Chris Wood, da Dominic Calbert-Lewin, da Jamie Bardy ne kadai suka kara shi.
Shi kuma dan wasa Taiwo Awoniyi ya fi kowanne dan kwallon Afirka shiga wasa daga baya a Forest, inda Jack Taylor na Ipswich ne kawai ya dara shi zama a bencin. Wasa 23 cikin 26 da dan Najeriyar ya buga ya shiga ne bayan fara wasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: abokan hamayya kwallo daga hamayya sau
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.
Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.
Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban.
A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.
Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.
Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.
Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.
Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.
Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.
Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.
Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.
A garin Chuwasu dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.
Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.
Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.
Yace da farko suna da shakku akan amfani da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.
Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.
Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.
A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.
A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.
Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.