Nijeriya Na Kan Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arziki Da Dawo Da Martabar Ƙasa — Ministan Yaɗa Labarai
Published: 14th, June 2025 GMT
Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.
Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban.
Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki.
“Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya.
“Martabar da Nijeriya ke da ita a baya tana dawowa sannu a hankali. Masu zuba jari suna samun ƙarin ƙwarin gwiwa a ƙasar.”
Ya ƙara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata sun wuce batun tattalin arziki kawai, domin suna gina tushe ne na cigaba mai ɗorewa, raba dama ga kowa, da ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Zhao Leji, ya kai ziyarar sada zumunta a kasar Kyrgyzstan daga ranar 23 zuwa 24 ga wata, inda ya gana da shugaban kasar Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov a birnin Bishkek.
Yayin ganawarsa da Japarov, Zhao Leji ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen tsakiyar Asiya ciki har da Kyrgyzstan, don inganta gina al’umma mai makoma bai daya tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya.
Japarov ya bayyana cewa, layin dogo tsakanin Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan, ba wai wata muhimmiyar hanyar sufuri ce kadai ba, har ma wata “hanyar abokantaka” ce dake sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin yankin.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp