Kwamandan  sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Amir Ali Haji Zadeh yana cikin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin da sojojin HKI su ka kawo wa  da asubahin yau Juma’a.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto majiyar juyin juya halin musulunci ta Iran tana tabbatar da shahadar Janar  Amir Ali Haji Zadeh.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas.

Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya

A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karbar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari.

“Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya dora daga inda ya tsaya a Legas.”

Sai dai Adebayo ya ce Tinubu ya yi kokari wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

“A bayyane yake cewa tattalin arzikin da Shugaba Buhari ya bari ba a tafiyar da shi yadda ya kamata ba, kuma yana cikin mawuyacin yanayi kamar na mara lafiya da aka kai dakin jinya. Kamar yadda likita ke bukatar yin cikakken bincike domin gano matsalar mara lafiyan, haka ma ake bukatar fahimtar matsalar tattalin arziki kafin a fara warkar da ita.

“Abin da Shugaba Tinubu ya yi shi ne ya daidaita marar lafiyan, amma ban tabbatar ko ya kai ga gano matsalar ba. Don haka mara lafiyar ba zai mutu nan da nan ba, amma kuma ba a samo maganin cutar shi ba.

“Ba a gano ciwon da ke damun mara lafiyan ba, amma a matsayinsa na likita, yana daukar wasu matakai. Wasu daga cikin matakan ma sun kara ciwon mara lafiyar, amma sannu a hankali likitan yana samun nasara a wasu bangarorin, wanda hakan ke sa wasu su yi tunanin cewa mara lafiyan na kan hanyar warkewa,” in ji Adebayo.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza.
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000