An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia
Published: 13th, June 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan ƙasar Australia ta kama wata ’yar asalin Najeriya da ke ƙasar Australia, Binta Abubakar bisa zarginta da safarar ɗalibai daga ƙasar Papua New Guinea tare da tilasta musu yin aikin da ba a biya a gonaki a faɗin jihar Ƙueensland da sunan bayar da tallafin karatu.
Binta mai shekara 56, an kama ta ne a ranar Laraba a filin jirgin saman Brisbane a lokacin da ta isa ƙasar Papua New Guinea, inda take zaune.
Kamen nata ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da ƙungiyar masu fataucin bil-Adama ta AFP ta yankin Arewa, wacce ta ƙaddamar da bincike kan ayyukanta a watan Yulin 2022 bayan samun bayanai daga ’yan sandan Ƙueensland.
A cewar AFP, “Wani gungun ‘yan asalin Papua New Guinea (PNG) da suka yi ƙaura zuwa Australia don yin karatu, an yi zargin cewa an tilasta musu yin aiki ba tare da son ransu ba a gonaki.”
An ba da rahoton cewa matar mai izinin zama ƙasashen biyu ta yaudari aƙalla ƴan ƙasar PNG 15, masu shekaru tsakanin 19 zuwa 35, zuwa Australia tsakanin Maris 2021 da Yuli 2023 ta hanyar kamfaninta, BIN Educational Serɓices and Consulting, da kuma ta hanyar ba da guraben karatu na bogi.
Rahoton ya bayyana cewa, shafin intanet na kamfaninta ya yi iƙirarin bayar da “daidaitaccen tsarin zamani don ilimi, horarwa da kuma aikin yi.”
Sai dai ’yan sandan sun ce gaskiyar lamarin ya sha bamban sosai.
Da zarar sun isa Australia, an yi zargin cewa an tilasta wa ɗaliban su sanya hannu kan jerin takaddun doka da ke tilasta su su biya kuɗin da ke da alaƙa da karatun, kuɗin jirgi, aikace-aikacen samar da biza, inshora da kuma kuɗaɗen doka.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Australia Safarar dalibai a Australia
এছাড়াও পড়ুন:
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoShugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.
Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.
Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.
Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.
NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.
Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.
Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.
Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.