Leadership News Hausa:
2025-09-17@21:53:13 GMT

Ƴansanda Sun Kama Shahararren Ɗan Damfarar Yanar Gizo A Bauchi

Published: 13th, June 2025 GMT

Ƴansanda Sun Kama Shahararren Ɗan Damfarar Yanar Gizo A Bauchi

Rundunar Ƴanandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Umar Yau, wanda aka fi sani da “Snake,” bisa zargin damfara ta yanar gizo da satar bayanan wasu mutane. An kama Yau, mai shekaru 25 daga unguwar Yelwan Makaranta a Bauchi, bayan binciken da aka fara sakamakon ƙorafi daga wata mata da ya damfara.

Fatimah Faiz Ali Bawahab, wata ’yar kasuwa ta yanar gizo, ta kai ƙorafin cewa wani ya ƙirƙiri asusun bogi a Facebook da sunanta da hotunanta don damfarar mutane. CSP Ahmed Wakil, kakakin rundunar, ya ce wanda ake zargin ya ƙirƙiri asusun “Amizeebaby Muhd” inda ya ke tallata kasuwancin ƙarya, yana karɓar kuɗi daga mutane ta asusun banki.

Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da Sarakuna Da Gundumomi Mataimakin Firaministan Sin Ya Gana Da Ministar Kudin Birtaniya

An gano cewa an taɓa damfarar wani Nafiu Muhd a watan Maris 2022, inda ya tura kudi zuwa asusun da ke dauke da suna Hansatu Yau, bayan haka aka toshe shi. Daga baya, bincike ya gano cewa ana amfani da sunayen Hansatu Yau da Umar Yau wajen karbar kuɗin jama’a a yanar gizo.

Bayan ƙorafin da aka samu, Kwamishinan ’Yansanda ya umurci gudanar da bincike na fasaha wanda ya kai ga kama Yau a ranar 5 ga Yuni, 2025. An kwato kati tara na ATM, katin zabe, na’urar MiFi, da sauran kayayyakin da suka tabbatar da laifin. Yau ya amsa cewa ya damfari mutane kusan 40 cikin shekaru biyar. An miƙa shi zuwa Rundunar ’Yansandan Kano don ci gaba da bincike da shari’a.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.

Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.

DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala

A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.

“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).

“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.

Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin