Leadership News Hausa:
2025-09-18@02:05:51 GMT

SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1

Published: 1st, March 2025 GMT

SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1

1.1 Abinci sahur yana da albarka; yin sahur albarka ne, haka ma abincin sahur abinci ne mai albarka.

Ana karɓo hadisi daga Miƙdãm ɗan Ma’adikarib Allah ya ƙara yarda a gare shi, daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Ina horonku da cin abincin sahur, domin abinci ne mai albarka” Nasã’i (Almujtabã 4/149 da Sunanul Kubrã 2/115) da Ahmad (Musnad #17192) da salsala ingantacciya.

An karɓo daga Abud Dardã’i Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Shi sahur abinci ne mai albarka.”Ibnu Hibban (Al’ihsãn #3464) Ɗabarãni (Mu’ujamul Kabir 17/131 hadisi mai lamba 322).

An karɓo daga Irbãdu ɗan Sãriyatu Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya gayyace ni cin abincin sahur a cikin Ramalana sai ya ce: ” Tawo ka ci abinci mai albarka” Abu Dãwud (#2344) da Nasã’i (Almujtabã 4/148) da Ibnu Hibbãn (Al’ihsãn #3465) salsalar hadisin ingantacciya ce. A lafazin Nasã’i ya zo da ce: Na ji Manzon Allah (S.A.W) Yana gayyatar mutane cin abincin sahur a cikin Ramalana…

1.3 Allah yana yabon masu yin sahur, Mala’iku kuma suna yi musu addu’a.

An barɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya ƙara yarda a gare su, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Lalle Allah yana yabon Mala’iku kuma suna addu’a ga waɗanda suke yin sahur” Ibnu Hibbãn (Al’ihsãn #3467) da Ɗabarani (Mu’ujamul Ausaɗ 6/287) da salsala ingantacciya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Ramadan Allah ya ƙara yarda a gare mai albarka

এছাড়াও পড়ুন:

An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin

Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.

Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.

Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.

Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II

“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.

Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.

Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.

Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.

Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren  ibada da gidajen marayu.

Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.

Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa