Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6
Published: 13th, June 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano ta musanta zargin da wasu ke yi cewa ta karɓo sabon bashi na dala miliyan 6.6 daga watan Yuni zuwa Disamba 2023, tana mai cewa wannan zargi ƙarya ne marar tushe da aka ƙirƙira domin ɓata mata suna. Wannan na zuwa ne bayan wata ƙungiyar siyasa mai suna APC Patriotic Volunteers ta yi zargin cewa gwamnatin NNPP mai ci a jihar ta karɓo bashi daga ƙasashen waje ba tare da bayyana hakan ba.
Darakta Janar na Ofishin Gudanar da Basussuka a jihar, Dr. Hamisu Sadi Ali, ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta hau mulki, ba ta karɓi wani sabon bashi ko na gida ko na waje ba, balle a ɓoye shi daga idon jama’a. Ya ce duk wani bashi da gwamnatin jihar ke aiki da shi a halin yanzu an gada ne daga gwamnatin da ta gabata.
Kocin Kano Pillars Usman Abdullahi Ya Ajiye Aikinsa Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A KanoDr. Ali ya kuma ƙalubalanci tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Usman Alhaji, wanda ya jagoranci ƙungiyar da ta yi zargin, yana mai cewa duk wanda ke da hujjar wannan zargi ya fito da takardun da ke tabbatar da hakan – ciki har da sunan mai bayar da bashin, kwafen yarjejeniyar, dalilin karɓa, da tsarin biyan bashin.
A cewarsa, akwai doka mai ƙarfi da ke kula da basussuka a jihar, wadda gwamnatin APC ta gabata ta kafa a 2021. Wannan doka ta bai wa ofishinsa ikon karɓar bashi cikin tsarin doka da cikakken sahihanci, kuma ba wani bashi da aka karɓa tun bayan 2023. Ya ce gwamnati na gudanar da harkokinta cikin gaskiya da rikon amana, kuma ba za ta lamunci ƙarya da siyasar ɓatanci ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da Sarakuna Da Gundumomi
A cewarsa, dukkanin takardar neman kirkirar sabon masarauta ko sarki ko gunduma dole ne a aike zuwa addireshin gwamnan jihar ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatar kananan hukumomi da kula da masarautu na jihar.
Kazalika, ya ce dole ne masu nema su gabatar da takaitaccen tarihin al’ummar da suke nema wa masarauta ko sarki ko gudunmawa tare da tarihin masarautar ko sarki ko gundumar da ke yankin da suke neman fita daga ciki.
Sanarwar ta kuma nemi a sanya dukkanin wani muhimmin bayanin da aka san zai iya taimakawa wajen la’akari da bukatar masu nema.
Har ila yau, sanarwar ta ce dole ne a takardar neman a samu sahihin sanya hannun hakimi, sarakunam kauye, da shugabannin al’umma tare da tabbacin wannan neman ta fito ne daga al’ummar wannan yankin da ake nema mata masarauta ko sarki ko gunduma.
Sanarwar ta kara da cewa duk al’ummomin da ke son kirkirar sabbin masarautu, sarakuna, ko gundumomi su na da dama kuma su na da ‘yancin gabatar da bukatar neman.
Gidado ya jaddada cewa shirin na daya daga cikin kudirin gwamnati na bunkasa gudanar da harkokin kananan hukumomi, da kiyaye al’adu, da karfafa cibiyoyin gargajiya a matsayin muhimman ginshikan zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba masu ma’ana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp