An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu
Published: 13th, June 2025 GMT
Hukumomin ’yan sandan Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarin da suke na daƙile munanan laifuka a ƙasar.
Na baya-bayan nan dai shi ne ceto mutanen da aka sace, da kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ƙwato manyan bindigogi da alburusai a jihohin Delta da Katsina.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce a jihar Katsina an samu gagarumar nasara a ranar 8 ga watan Yunin 2025, inda haɗin gwiwar JTF da suka haɗa da jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suka daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane a hanyar ƙauyen Danmusa zuwa Mara Dangeza a ƙaramar hukumar Danmusa.
Adejobi ya ce hakan na iya yiwuwa ne ta hanyar shigar da wasu gungun ’yan bindiga da suka yi yunƙurin guduwa da waɗanda aka yi garkuwa da su a wani artabu da ya kai ga ceto mutum 11.
Nasarar da aka samu yankin Kudu maso KuduA halin da ake ciki kuma, a yankin Kudu maso Kudu, Jihar Delta, hukumar ’yan sanda ta kama wani Abubakar Hassan, wanda babban wanda ake zargi da aikata laifin satar mutane ne a tsakanin jihohin Delta da Ribas da Imo, da Enugu.
Jami’an da ke da alaƙa da samun nasarar sun yi hakan ne yayin da suke aiki da sahihan bayanai.
A yayin da ake yi masa tambayoyi, Hassan ya bayyana cewa shi ne ya jagoranci gudanar da hari a yankin Ughelli-Ozoro na jihar mai arzikin man fetur.
Ya kuma jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa maɓoyarsa a wani daji da ke Ozoro. A can jami’an sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da tarin alburusai huɗu da harsashi guda talatin da biyu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA