Leadership News Hausa:
2025-09-17@23:11:22 GMT

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

Published: 14th, June 2025 GMT

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

Haka zalika koda ba ki fuskanci matsalar zubar jini ba, ki daure ki shayar da jaririnki hakan zai ci gaba da sa mahaifarki harbawa ta taso daga mararki ta koma kasan cikinki cikin sati 2 da haihuwa, hakan zai rage miki tsananin ciwon mara duk da shayarwa akwai zafi wani lokacin.

Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa Insha Allahu

 

Daga kanmu, magana ta ƙare.

Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin

Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.  

An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.

Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.

Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.

Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa

Ya ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.

Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.

AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.

Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.

Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Bida Poly ta kawo sojoji su kula da jarrabawar ɗalibai
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
  • Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin