Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Gina Kasa A Gabar Da Ake Bikin Cika Shekaru 120 Da Haihuwar Dan Mazan Jiya Chen Yun
Published: 14th, June 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a yi koyi daga akidun dan mazan jiya, kuma jagora na gari Chen Yun, tare da kara azamar dorar da kyawawan dabi’unsa cikin himma da kwazo, don gina kasar Sin mai matukar karfi.
Shugaba Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar, ya yi kiran ne a yau Juma’a, cikin jawabin da ya gabatar, yayin taron bikin murnar cika shekaru 120 da haihuwar Chen Yun, taron da ya gudana a babban dakin taruwar jama’a dake tsakiyar birnin Beijing
Shugaban na Sin ya ce, an haifi Chen a shekarar 1905, ya kuma shiga JKS a shekarar 1925.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp