Iran : harin da Isra’ila ta kai ‘ ayyana yaki’ ne_ Araghchi
Published: 14th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka a kan kasar tamkar shelanta yaki ne.
Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa babban sakatare na MDD da kuma shugaban kwamitin sulhu bayan da Isra’ila ta kai munanan hare-hare kan wuraren soji da cibiyoyin nukiliya da kuma wuraren zama wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), masana kimiyyar nukiliya da fararen hula na iran.
“Wadannan ayyuka na zalunci ba wai kawai sun zama babban cin zarafi ne ga ‘yancin kan kasar Iran a matsayinta na mamba mai cin gashin kanta a Majalisar Dinkin Duniya ba, amma kamar yadda dokokin kasa da kasa da dokokin jin kai na duniya, ciki har da yarjejeniyar Geneva, suka tanada wannan na daga cikin ayyukan wuce gona da iri da laifukan yaki.”
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya sauke nauyin da ke wuyansa, ya yi kakkausar suka ga wannan ta’addanci tare da daukar matakin gaggawa kan Isra’ila.
Ya kara da cewa “Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi aiki da cikakkiyar azama wajen kare ‘yancinta, al’ummarta da kuma tsaron kasarta. Wannan wani hakki ne da ba za a iya tattaunawa da shi ba.”
Daga cikin hare-haren da ta kai, Isra’ila ta kai hari kan Cibiyar Nukiliya ta Natanz da ke tsakiyar kasar Iran, wadda ke aiki karkashin cikakken kulawar Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), in ji shi.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi gargadin cewa hare-haren ta’addanci na gwamnatin Tel Aviv na jefa rayuwar fararen hular Iran cikin hadari tare da haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Bakai’i: Iran Tana Son Ganin An Yi Taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa;Yunwar da mutanen Gaza suke fama da ita na tsawon watanni biyar, laifi ne maras tamka da HKI take tafkawa, da ya zama wajibi kungiyar kasashen musulmi ta yi taron gaggawa akansa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Dr. Isma’ila Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya kuma yi Magana akan tattaunawar da Iran ta yi da kasashen turai akan shirinta na makamin Nukiliya, ya ce: Tattaunawar da aka yi ta da kasashen turai manufarta ita ce dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata akan shirinta na Nukiliya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Kasashen na turai ba su da hakkin su kakabawa Iran takunkumi, idan kuwa har su ka ci gaba to za su fuskanci mayar da martanin Iran.