Gwamnatin Tarayya Ta Dukufa Wajen Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
Published: 13th, June 2025 GMT
Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan.
Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa.
Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.”
A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai miliyan 400 a nan da shekarar 2050, Kyari ya ce gwamnati ta dukufa wajen kyautata harkar noma da kuma samar wa matasa ayyukan yi a matsayin mataki mai dogon zango na samar da wadatar abincin.
Ya ce gwamnati na kuma kokarin gyara kadarorin da kasar ke da su kamar su taraktoci, da sauran muhimman kayan aiki domin kara bunkasa samar da abinci.
Ya kuma ce Nijeriya ta yi hadin gwiwa da kasar Belarus don samar da ayyukan hadaka da nufin kara yawan kayan da ake fitarwa.
Ministan ya yi gargadin cewa a guji amfani da injinan noma da gwamnati ta samar ba ta hanyoyin da suka dace ba, inda ya bukaci manoma da su yi amfani da irin wadannan kayan aikin yadda ya kamata.
Ministan ya ce warare uku na ajiyar kaya wato silo ne kawai suke aiki a halin yanzu, inda ya sha alwashin cewa za a maida hankali wajen gyara sauran.
Kyari ya ce “Ma’aikatar noma da dawata kasa da abinci za ta hada kai da masu ruwa da tsaki don tabbatar da an yi amfani da wadannan muhimman wuraren ajiyar kaya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.