Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)
Published: 14th, June 2025 GMT
Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda za’a kubuta daga irin cin fuskar da ake yi kowace rana.
Kafin dai a tsunduma sosai cikin lamarin cinikin Bayi, yana da matukar kyau a fara yin bayani kan yadda abin ya fara:Lamarin cinikin Bayi ba manufa bace ta Yammacin Turai.Duk lamarin ya zarce wani hasashen da za’a iya yi ko wani rubutun,da aka yi aka aje.Idan kuma aka duba ta bangaren nahiyar Afirka ita kanta, sha’anin cinikin Bayi ya kasance nae kafin zuwa Turawa shekaru darurra da suka gabata,lamarin kuma yana ci gaba har zuwa halin da ake ciki yanzu ,ana iya tunawa da yadda Bayin da aka saya a nahiyar Afirka ake tafiya da su ta hanyar Sahara wadda take da Yashi,ta haka ne aka fara musanyar mutane,a bada su ,sannan a amshi wasu abubuwa”.
Afirka, a matsayinta na nahiya ita ma ta dandana kudarta idan ana maganatr cinikin Bayi har zuwa shenture 14 wanda ya zarce shekara 1000 ke nan:10 ga duniyar Larabawa,sai kuma 4 ga sauran yammacin Turai. Ciniki Bayi na bangaren Larabawa ya far ne a karni na 8 hakan ta kasance ne saboda yadda addinin musulunci ya hana Musulmai daga bautar da ‘yan’uwansu. Duk da an hana hakan bukatar mutane su rika yin wasu ayyuka,don haka shi yasa Larabawa suke zuwa nahiyar Afirka domin su samu Bayin.Da farko sun tsaya ta gabas ta gabar ruwa na, Rift Balley, amma yayin da suke kasuwanci, sai suka rika yada addininsu na musulunci. Wannan ya nuan ke nan wurin da yake ana ta lamarin fataucin Bayi,ya zama yanzu babu yadda za su yi su samu Bayi daga can,don haka sannu a hankali sai suka maida akalarsu zuwa yammacin Afirka.domin idon su ya fara budewa saboda ai addinin musulunci ya hana cinikin Bayi. Wannan shi yake nuna duk yadda Larabawa suke bukatar samun ‘yan Afirka a matsayin Bayi ya zo karshe.
Abu daya wanda yake kamar sun yi kama da juna tsakaanin Larabawa da Yammacin Turai shi ne suna yin amfani ne da addini, Musulunci da Kiristanci domin su samu bakin bada dalilin da yasa suke kasuwancin mutane.A kokarin da muke na nuna yin kama da juna, sai mun yi bayani dangane da bambancin, tsakanin kasuwancin na hanyar da ake bi ta Yashi, da kuma ta wani babban Kogi da kuma na ake bi ta babban ruwa ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: cinikin Bayi
এছাড়াও পড়ুন:
Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata
Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya.
Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji.
Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani.
A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa.
Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga don shiga tsakani amma ya faɗi sumamme a yayin.
Ayuba, wanda aka yi imanin yana cikin koshin lafiya kafin faruwar lamarin, an garzaya da shi asibiti a garin Gawu, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsa.
Sarkin yankin, bayan samun labarin lamarin, ya sanar da ’yan banga tare da ba da umarnin kama ma’auratan, waɗanda daga baya aka mika su ga jami’an tsaro a Gawu.
Ibrahim, daya daga cikin ’yan bangan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, “Mun fahimci cewa ƙaramar rashin fahimta ce kawai ta kai ga faɗan tsakanin makwabcin mamacin da matarsa.”
Ya ƙara da cewa an kai gawar mamacin kauyensa na Paiko a Jihar Neja don binnewa.
’Yan sanda a yankin Gawu sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce har yanzu ana ci gaba da bincike.