Harin Isra’ila a kan Iran ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zama dar-dar
Published: 13th, June 2025 GMT
An shiga yanayin zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya bayan wasu munana hare-hare da Isra’ila ta kaddamar a kan tashoshin Nukiliya da manyan sojojin Iran a ranar Alhamis.
Hukumomin Isra’ila dai sun tabbatar da kai harin inda suka ce ya kunshi daruruwan jirage kan abin da suka kira da kololuwar wurin hada makaman Nukiliya na Iran da kuma manyan sojojinta.
Daga cikin manyan mutanen da ake zargin harin ya hallaka har da Manjo-Janar Hossein Salami, Shugaban Rundunar IRGC ta Iran da wasu manyan kwamandoji da manyan masana a tashar Nukiliyar.
Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta sanar da cewa jiragen yaki sama da 200 ne suka yi aikin kai hare-haren kuma sun kai su ne a muhimman wurare sama da 100 a Iran.
Sai dai jim kadan bayan labarin kai harin, Iran ta mayar da martani.
Kafofin yada labaran gwamnatin kasar sun rawaito cewa Iran ta harba jirage marasa matuka sama da 100 da suke hakon wurare daban-daban a cikin Isra’ila.
Kazalika, Shugaban addini na kasar, Ayatollah Ali Khomenei ya sha alwashin sai Isra’ila ta dandana kudarta.
Tuni rahotanni daga Isra’ila suka nuna yadda mutane suka shiga sayayya a kasuwanni ba ji ba gani suna adanawa saboda gudun abin da zai faru na martani.
Wasu hotuna da kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP) ya wallafa sun nuna tituna a biranen Tel Aviv da Kudus sun dade.
Lamarin dai ya sa an soke tashi da saukar jirage zuwa kasashe da dama na yankin na Gabas ta Tsakiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?
Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba.
Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin Syriya ta yi kan karakainar da jiragen yaki da makamai masu linzami ke yi a sararin samaniyar kasar.
Wani mai sharhi ya fada wa Enab cewa gwamnatin Syriya ta yanke shawarar tsayawa tsakiya kan lamarin ne kasancewar tana daukar Isra’ila da Iran a matsayin abokan gabarta.
Ya ce: “Babu daya daga cikinsu da za ka bayyana shi a matsayin abokin al’ummar Syriya, kuma dukkaninsu sun taka rawa wajen lalata kasar Syriya.”
Iran na daga cikin manyan kasashen da suka taimaka wa tsohon shugaban Syriya Bashar al-Assad, ita kuma Isra’ila ta kaddamar da daruruwan hare-hare ta sama kan Syriya, kuma ta jibge sojojinta a yankunan tudun mun tsira tun cikin watan Disamba bayan tuntsurar da gwamnatin Assad.
Ya ce gwamnatin Syria a yanzu ta shagalta ne da kokarin daidaita lamurra a cikin gida da kuma karfafa dakon dangantakarta da Turkiyya da kuma kasashen yankin Gulf.
Jaridar da ke kare muradun yankin Larabawa ta ‘Middle East Eye’ ta ruwaito cewa shugaban Turkiyya Receb Tayyib Erdogan ne ya shawarci sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa cewa kada ya tsoma kansa cikin rikicin.
Saba ka’idar sararin samaniya
Kafar yada labarai ta Syria ta buga rahotanni da dama tana cewa Isra’ila da Iran na karya ka’idojin amfani da sararin samaniyarta, inda ta ce jirage marasa matuka da kuma makamai masu linzami da dama sun fada cikin kasar.
Kafar yada labarai ta Syria – SANA – ta ruwaito cewa wani jirgi mara matuki ya fada kan wani gida a birnin Tartus, kuma daga baya an tabbatar da cewa matar ta rasu sanadiyyar raunukan da ta samu.
Haka nan kafar yada labaran ta SANA ta ruwaito cewa wasu jirage marasa matuka sun fada kan gidajen al’umma a birnin Daraa kuma wani makamai mai linzami ya fada gefen Damascus, babban birnin kasar, inda makamin ya bar wani katon rami.
Sai dai shirun da gwamnatin Syria ta yi kan wannan lamari ya ja hankalin kafafen yada labarai a cikin kasar da kuma kasashen Larabawa.
Yawancin jaridun sun ja hankalin al’ummar kasar cewa kada su kusanci wauraren da makaman ke fadawa.
Sai dai wata majiya ta gwamnati ta karyata ikirarin jaridar Al-Watan, wadda ta ce Ahmed al-Sharaa ya amince wa Isra’ila ta yi amfani da sararin samaniyar Syria wajen samun bayanai kan tafiyar makaman da Iran ke harbawa.
Gidan talabijin na Syria TD da ke da mazauni a Turkiyya ya tattauna da wani mai sharhi, wanda ya ce ya kamata Syria ta kai korafin wajen Majalisar Dinkin Duniya, sannan kuma ta yi amfani da kasashe kawayenta wajen hana karya ka’idojin amfani da sararin samaniyarta.
Gidan talabijin dain ya ce yakin na Iran da Isra’ila ya yi cikas ga zirga-zirgar jirage zuwa kasar da kuma datse kai tallafi ga al’ummar kasar masu bukata.
Wata jarida ta yankin Larabawa, Al-Kuds Al-Arabi ta ce akwia damuwa kan cewa yakin zai kara raunana tattalin arzikin Syria wanda ba ya da karfi, inda ta ce darajar kudin kasar ta Syria ya fadi da kashi 10 cikin dari tun bayan fara yakin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp