Aminiya:
2025-06-14@09:12:28 GMT

Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi

Published: 13th, June 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matsayin cin ribar cikakkiyar dimokuraɗiyya ba, duk da cewa an dawo mulkin farar hula shekaru 26 da suka gabata.

Yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, Fayemi ya bayyana cewa duk da cewa ana gudanar da zaɓe a kai a kai a ƙasar, har yanzu an rasa muhimman abubuwan da suka kamata su kasance a tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya.

Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna

“Bai kamata mu rikita gudanar da zaɓe da aiwatar da dimokuraɗiyya ba,” in ji shi.

“Abin da muka samu a 1999 shi ne ’yancin zaɓar shugabanni, amma hakan kawai ɓangare ne guda ɗaya.

“Abin da muke da shi mulkin farar hula ne, ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba.”

Ya ce an samu ci gaba a ƙarƙashin gwamnatoci daban-daban tun daga baya, amma har yanzu Najeriya na buƙatar ƙarfafa al’adar dimokuraɗiyya da sauye-sauyen da suka dace.

Fayemi ya kuma tuna da lokacin da ya kasance ɗaya daga cikin masu fafutukar dimokuraɗiyya a zamanin mulkin soja, musamman a lokacin marigayi Janar Sani Abacha.

Ya bayyana yadda suka gudanar da shirye-shirye a wani gidan rediyo a aka ɓoye, don ƙalubalantar gwamnatin soji.

“Ba wai rashin tsoro ba ne, mun san hatsarin da ke tattare da lamarin, amma mun yi imani da abin da muke yi,” in ji shi.

“Na taɓa ɗaukar na’urar watsa shirye-shiryen rediyon Kudirat a cikin jirgin Air France da ya sauka a Legas lokacin da fafutukar ta yi zafi. Wannan kaɗai na iya jefa ni cikin hatsari.”

Ya ce waɗanda suka mutu a lokacin ba don sakaci suka rasa rayukansu ba, sai don sun gaskata ƙudurinsu na ganin an samu ’yanci.

Fayemi ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa karrama wasu daga cikin waɗanda suka fafata wajen dawo da dimokuraɗiyya.

Sai dai ya nuna damuwa cewa wasu da dama da suka taka muhimmiyar rawa a bayan fage ba a karrama su ba.

“Mutane da dama sun sa rayuwarsu cikin hatsari. Su ma sun cancanci a yaba musu.

“Ba daidai ba ne a girmama waɗanda ake gani a manta da waɗanda suka bayar da gudunmawarsu a bayan fage.”

Maganganun Fayemi sun haifar da zazzafar muhawara kan yadda Najeriya ke da buƙatar ci gaba kafin a kira ta da ƙasar da ke da cikakkiyar dimokuraɗiyya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Dimokuraɗiyya Fayemi gwagwarmaya Najeriya dimokuraɗiyya ba

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi.

Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi.

NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya

Wadansu dalilai ne ke kara kawo rashin aikin yi a Najeriya?
Wadansu hanyoyi za’a bi wajen magance rashin aikin yi?
Wadannan da ma wasu tambayoyi na cikin batutuwan da Shirin Najeriya A Yau zai yi duba akai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
  • Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
  • Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
  • 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya
  • NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya?
  • Iran ta Yi Gargadin Cewa Zata Fice Daga Yarjeniyar NPT Idan Hukumar IAEA Ta Tir Da Ita
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 8 A Jihar Filato
  • Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya
  • Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi