‘Yan Wasa Biyar Da Suka Taka Rawar Gani A Kofin Zakarun Turai
Published: 15th, June 2025 GMT
Sannan shi ne ya fi kowanne danwasa yunkurin cin kwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23.
Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45.
Rapinha
Zakakurin danwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin ‘yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki daya – ba a Champions League ba kawai.
Rapinha mai shekara 28 ya ci ƙwallo tara da ƙafarsa ta hagu, uku da dama, da kuma ɗaya da kansa. Huɗu daga cikin ƙwallayen da ya ci daga wajen yadi na 18 ne.
Wani abu da ya kamata a lura da shi shi ne babu bugun finareti ko ɗaya cikin ƙwallayen da ya ci a wasa 14 da ya buga.
Lamine Yamal
Duniya ta fara maganar dan wasa kuma matashin da ya fi birge ‘yankallo ko shakka babu shi ne Lamine Yamal na Barcelona. Dan wasan na Sifaniyan mai shekara 17 ya taka rawar gani cikin wasanni 13 da hya buga wa kungiyar, inda ya kai hare-hare har sau 52. Daga cikinsu akwai munana 25. Yamal ya ci kwallo biyar sannan ya bayar da uku aka zira a raga. Sannan ya yi nasarar yanka abokan hamayya har sau 109 a gasar, wadda ita ce ta biyu da ya buga wa Barcelona.
Serhou Guirassy
Shima dan wasa Serhou Guirassy wani danwasan da ya taka rawar gani a kakar da aka kammala shi ne Serhou Guirassy na Burossia Dortmund da kuma Faransa. Danwasan mai shekara 29 ya jefa kwallaye har 13 a raga – iri daya da na Rapinha – sannan ya bayar gudummawa aka ci wasu hudu cikin wasa 14. Cikin kwallayen da ya ci har da uku rigis ya dura wa Barcelona a wasa na biyu na zagayen kusa da na kusa da na karshe.
Harry Kane
Danwasan gaba na Bayern Munich kuma kyaftin ɗin Ingila ya ɗora kan abin da ya saba, inda bai gushe ba sai da ya zira kwallaye 11 cikin wasanni 13 da ya buga wa kungiyar, kazalika, Kane mai shekara 31 ya kai hare-hare 49, cikinsu akwai masu hadari 25. Haka nan, ya bayar da kwallo biyu an zira a raga kafin Inter Milan ta yi waje da su daga gasar a zagayen kusa da na karshe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Serhou Guirassy mai shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Kakkabo Jiragen Yakin Isra’ila Biyu Kirar F-35
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta harbo jiragen saman yaki kirar F-35
Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta yi nasarar harbo jiragen yaki kirar F-35, bayan da ta yi nasarar auna wasu jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kirar F-35 guda biyu, kuma ta barar da su kasa.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da wadannan jirage masu tsananin ci gaban zamani wajen kai hare-haren wuce gona gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da safiyar ranar Juma’a, wanda hare-haren suka yi sanadiyyar shahadar wasu manyan jami’an sojan Iran da masana kimiyyar nukiliya da fararen hula da suka hada da mata da kananan yara.
Ma’aikatar hulda da jama’a ta rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Dakarun tsaron saman Iran sun harbo jiragen saman yaki kirar F-35 guda biyu, baya ga wasu jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya marasa matuka ciki.
Sanarwar ta nuna cewa: Jami’an tsaron Iran sun kame daya daga cikin matukan jiragen wacce mace ce, kuma ana kan bincike domin sanin makomar matukin daya jirgin.
Abin lura shi ne cewa: Jiragen yakin kirar F-35 da ‘yan sahayoniyya ke amfani da su na daga cikin wadanda suka ci gaba a duniya kuma ake gwada su.