DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci
Published: 14th, June 2025 GMT
Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta ƙasa ta dakatar da shirinta na gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku, bayan martani mai zafi daga jama’a. Tun da farko, an tsara addu’ar ne domin neman taimakon Ubangiji wajen tabbatar da tsaron (wadataccen) abinci a Nijeriya.
Wata takarda da ta bayyana ga jama’a, wadda Daraktar Gudanarwa ta Ma’aikatar, Mrs.
Sai dai cikin wata sabuwar sanarwa daga wannan darakta, an bayyana cewa an dakatar da shirin addu’ar har sai wani lokaci na gaba, ba tare da bayyana dalilin janye umurnin ba. Wannan matakin ya biyo bayan suka da jama’a suka yi a kafafen sada zumunta kan dacewar shirin.
Masu sukar sun bayyana cewa gwamnati ya kamata ta mai da hankali wajen samar da tsare-tsare na zahiri kamar gyaran dabarun noma, da tallafawa manoma da kuma inganta rarraba abinci, maimakon dogaro da addu’a wajen shawo kan matsalar yunwa da hauhawar farashin abinci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza.
Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay au Litinin.
Alhayya ya bayyana cewa akwai ci gaba a tattaunawar tsagaiuta wuta tsakanin kungiyar da HKI da kuma Amurka, amma janyewar HKI da kuma Amurka a wannan tattaunawar wata dasisa ce don ci gaba da kissan kiyashi a gaza.
Ya ce: masu shiga tsakanin sun tabbatar da cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake yi a doha, sai dai sun janye ne don samun lokacinda da zasu gaggauta kissan Falasdinawa a Gaza, don cimma mummunan manufofinsu a gaza.
Dangane da rabon kayakin agaji wanda HKI da Amurska suka shira kuma Alhayya ya yi allawadai da shi ya kuma kara da cewa cibiyoyin bada agajin tarko ne na kara kissan Falasdinawa a Gaza.
Ya kara da cewa shirin GHF na Amurka da kuma HKI shiri ne na kissan karin Falasdinawa bayan sun sanyasu cikin yunwa na kimani watanni biyu kafin su fara rabon abinda suke kira agaji.