Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da Sarakuna Da Gundumomi
Published: 13th, June 2025 GMT
A cewarsa, dukkanin takardar neman kirkirar sabon masarauta ko sarki ko gunduma dole ne a aike zuwa addireshin gwamnan jihar ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatar kananan hukumomi da kula da masarautu na jihar.
Kazalika, ya ce dole ne masu nema su gabatar da takaitaccen tarihin al’ummar da suke nema wa masarauta ko sarki ko gudunmawa tare da tarihin masarautar ko sarki ko gundumar da ke yankin da suke neman fita daga ciki.
Sanarwar ta kuma nemi a sanya dukkanin wani muhimmin bayanin da aka san zai iya taimakawa wajen la’akari da bukatar masu nema.
Har ila yau, sanarwar ta ce dole ne a takardar neman a samu sahihin sanya hannun hakimi, sarakunam kauye, da shugabannin al’umma tare da tabbacin wannan neman ta fito ne daga al’ummar wannan yankin da ake nema mata masarauta ko sarki ko gunduma.
Sanarwar ta kara da cewa duk al’ummomin da ke son kirkirar sabbin masarautu, sarakuna, ko gundumomi su na da dama kuma su na da ‘yancin gabatar da bukatar neman.
Gidado ya jaddada cewa shirin na daya daga cikin kudirin gwamnati na bunkasa gudanar da harkokin kananan hukumomi, da kiyaye al’adu, da karfafa cibiyoyin gargajiya a matsayin muhimman ginshikan zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba masu ma’ana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ko sarki ko
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido.
An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje.
Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar da ingantaccen kulawa.
A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta dauki nauyin kula da lafiyar ido ga mutum sama da 500 daga Birnin Kano da sauran kananan hukumomi.
Shugaban kula da lafiya am matakin farko na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Jafar, ya ce wadanda lalurar su ba ta tsananta ba za a ba su shawarwarin kula da lafiyar su, da magunguna, wa su ma har da tabarau, yayin da wadanda ta su ta tsananta kuma za a musu tiyata.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiya tare da yi wa gwamnati addu’a don samun nasara.
Shugaban tawagar likitocin, Dr. Kamal Saleh, ya tabbatar da cewa shirin ya samu nasara sosai.
Daga Khadijah Aliyu