Trump ya dakatar da kamen baƙin haure a wasu wurare na Amurka
Published: 15th, June 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci jami’an hukumar kula da shige-da-ficen-kasar da su dakatar da aikin samamen kama baƙin-haure ’yan ci-rani, a gonaki da otal-otal da ma gidajen sayar da abinci na fadin kasar.
Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito ma’aikatar tsaron cikin gida na tabbatar da samun umarnin, wanda aka mika shi ga hukumar kula da shige-da-fice da kuma ta yaki da fasa-kwauri, to sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai kai ga tabbatar da sahihancin umarnin ba.
Tun a lokacin yakin neman zaben shugabancin Amurka zango na biyu ,Mista Trump ya alkawarta korar bakin-hauren da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
To sai dai wannan mataki ya fuskanci kakkausan suka sakamakon yadda ake kame mutanen da ba su taba aikata laifin komai ba, musamman wadanda ke aiki a gonaki da sauran wurare, lamarin da ya janyo barkewar zanga-zanga a wasu sassan kasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kawo yanzu an shafe kwanaki ana tarzoma a birnin Los Angeles na Jihar California ta Amurka, inda masu zanga-zanga ke dauki-ba-dadi da dakarun tsaron kasa da Shugaba Trump ya tura tun farko domin kwantar da zanga-zangar da ta barke sakamakon kamen bakin haure.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar.
Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su ne ci gaba da zama ginshikin dangantakar ƙasashenmu biyu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp