Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya
Published: 13th, June 2025 GMT
Duk da cewa, yanayin zafi ya yawaita a kasar ta Saudiyya, yayin gudanar da aikin Hajjin 2025, koda-yake; akasarin wadanda suka mutu daga Nijeriyar tsofaffi ne.
Rasuwar farko da aka sanar ta wani Alhaji ce daga Jihar Oyo, Alhaji Sulaimon Hamzat, wanda ya rasu a ranar 17 ga Mayun 2025 a kasar ta Saudiyya.
Na biye da shi kuma daga Jihar Abiya ne, mai suna Alhaji Saleh, Shugaban Kasuwar Shanu ta Lokpanta, wanda ya rasu a garin Makka a daren ranar Litinin 26 ga watan Mayun 2025.
Bayan haka kuma, sai wata Hajiya mai shekaru 75 daga Jattu Uzairue a Karamar Hukumar Etsako ta yamma da ke Jihar Edo, Adizatu Dazumi, wadda ta mutu a ranar Litinin 26 ga Mayun 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya.
An samu rahoton cewa, Dazumi ta kamu da rashin lafiya jim kadan bayan kammala dawafi, inda aka garzaya ta ita zuwa asibitin Sarki Fahad da ke Makka a ranar Lahadi, washegari kuma ta mutu.
Haka zalika, wata Hajiya daga Jihar Filato ta rasu a birnin Makka da ke Saudiyya, yayin gudanar da wannan aiki Hajjin 2025.
Marigayiyar, mai suna Hajiya Jamila Muhammad, ta rasu ne sakamakon cutar Siga da ke fama da shi a asibitin Sarki Abdul’aziz da ke birnin Makka.
Kwana daya kafin fara aikin Hajjin 2025, wani Alhaji daga Jihar Kano mai suna Shu’aibu Jibrin, ya rasu a garin Makka.
Haka nan kuma, wani Alhajin Nijeriya ya rasu a filin Arfa.
A cewar Shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, “Mun samu labari mara dadi cewa; mun rasa mahajjatanmu a yau Arfat, dayan kuma ya rasu kafin mu bar Makka,” in ji shi.
Ya kuma ce, mutuwar Alhazan daga Allah ne; inda ya kawar da rade-radin da ake yin a cewa, zafin rana ne ya haddasa su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.
Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar Asabar.
Kifewar kwalekwalen ta auku ne a sakamakon karonsa da wani kututture bayan ya ɗauki fasinjojin daga yankin Guni zai kai su kasuwar mako-mako da ke yankin Zumba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro.
Manajan Hukumar Albarkatun Koguna ta Ƙasa (NIWA), mai kula da yankin, Akapo Adeboye, ya ce an gano gwawar mutum 15, amma ana ci gaba neman wasu mutum uku, ko da yake cewa an yi nasarar ceto mutum 26 da ke sanye da rigunan kariya da ransu, bayan aukuwar hatsarin.
HOTUNA: Yadda Aisha ta koma gidan Buhari na Kaduna NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INECAdebayo ya bayyana cewa, “Mutanen sun taso ne daga ƙauyen Shayita za su tafi Kasuwar Kwata da ke Zumba tare da kayansu na miliyoyin kuɗaɗe a ranar Asabar 26 ga watan Yuli, 2025.
“Jami’an NIWA sun gudanar da aikin ceto, amma an samu asarar rayuka 18, an ceto wasu 26, kuma aka ci gaba da aiki da kuma ƙoƙarin kamo mai kwalekwalen.”
Shaidu sun ce hastarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na ranar Asabar, kuma yawancin fasinjojin mata ne da ƙananan yara, kuma jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) sun tabbatar da hakan.
Sarkin Ruwan Zumba, Umar Isah, ya ce mutum 15 ne suka rasu, an ceto 25, amma an yi asarar shanu uku da buhu 60 na shansherar shinkafa.
“A cikin mutum 15 da suka rasu har da ƙananan yara uku mata da gano gawarwakinsu,” in ji shi.
Amma Darakta Janar na Hukumar NSEMA, Abdullahi Baba Arah, ya ce gawa 13 aka gano kuma an yi jana’izarsu a ranar Lahadi.
Arah, wanda ya tabbatar da asarar wasu mutane da dabbobi da kayan abinci a hatsarin, ya ce gawarwakin sun haɗa da mata takwas da maza uku da kuma yara biyu.