Ƴansanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ceto Mutane 11 A Delta Da Katsina
Published: 13th, June 2025 GMT
Rundunar Ƴansandan Nijeriya, tare da haɗin gwuiwar sauran hukumomin tsaro, ta samu nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ceto mutane 11 da aka sace a jihohin Delta da Katsina. Wannan na cikin ƙoƙarin ci gaba da yaƙi da miyagun laifuka a faɗin ƙasa.
A jihar Katsina, an daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane a ranar 8 ga Yuni, 2025, a hanyar Danmusa zuwa Mara Dangeza, inda jami’an haɗin gwuiwa suka yi artabu da ‘yan bindiga.
A jihar Delta, jami’an CP-Special Assignment sun cafke wani Abubakar Hassan, wanda ake zargin jagoran gungun masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a jihohi da dama. Bayan gudanar da bincike, ya jagoranci jami’ai zuwa maboyarsu a dajin Ozoro, inda aka ƙwato bindigogi AK-47 guda biyu da harsasai. Hakanan, wani direba, Obi Ezekiel, ya shiga hannu yayin da aka gano bindiga ƙirar gida da alburusai a motarsa.
Babban Sufeton Ƴansanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya yaba da ƙwarewa da kwazon jami’an tsaro a waɗannan ayyuka, tare da jan hankali cewa rundunar zata ci gaba da gudanar da irin wadannan farmaki don tabbatar da cewa babu mafaka ga masu aikata laifi a duk faɗin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki
A jiya Talata ne dai aka zartar da hukuncin kisa akan wani babban jami’in Banki na gwamnati bayan da aka same shi da laifin barnata dukiya.
Kafafen watsa labarun kasar China sun ce mutumin da aka zartarwa da hukuncin kisan, tsohon manaja ne a wani babban kamfani na hukuma.
A shekarar 2024 ne dai aka sami Bay Tian Hua, saboda samunsa da karbar toshiyar baki da ta kai dalar Amurka miliyan 156 domin bai wa wani kamfani fifiko samun kwangilar aiki a tsakanin 2014-2018.
Tashar talabijin din CCTV ta gwamnatin kasar China ta ce; kotun al’umma ce ta yanke hukuncin akan wannan laifin da ta bayyana da cewa mai matukar hatsari ne.
An zartar da hukuncin kisan ne dai akan Bay a garin Tianjin dake yankin arewa maso gabashin kasar, bayan da ya yi bankwana da ‘yan’uwansa.
A kasar China dai ana zartar da hukuncin kisa akan wadanda aka samu dacin hanci da rashawa. Wasu lokutan kuma ana rage hukuncin kisan zuwa zaman kurkuku na shekaru biyu, ko kuma zaman kurkuku na har abada.
Kamfani da Bay ya yi wa manaja yana cikin manyan cibiyoyin kudi na bayar da bashi mai rassa a fadin kasar ta China.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran December 10, 2025 Antoni Gutress Ya Yi Allawadai Da Kutsen Da “Isra’ila” Ta Yi A Cibiyar Unrwa December 10, 2025 Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu December 9, 2025 Faransa ta ce da hannunta aka dakile juyin mulki a Benin December 9, 2025 RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne December 9, 2025 An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza December 9, 2025 Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon December 9, 2025 Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine December 9, 2025 Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba December 9, 2025 Najeriya : Matsala ce ta sa jirgin sojinmu yin saukar gaggawa A Burkina Faso December 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci