Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu
Published: 5th, July 2025 GMT
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Gani suke ai in su nuna suna samu kamar matan nasu za su dora musu hidima da yawa, sun gwamma ce su bar matansu da wahala. Wani ma dan rashin imani kokari yake ita matar ta ciyar da shi alhalin yana da damar sa, shi ya sa ko yaran wani lokaci in suka taso komai na mahaifiyarsu sai daga baya ya zo ana da-na-sani mara amfani a lokaci da ba shi da amfani.
Sunana Aisha Lawan Ya’u, daga Jihar Kano Ado Bayero Layout:
Dalilan da ya sa maza suke boyewa matansu samunsu: gaskiya san zuciya ne da rashin sanin yakamata, duk namiji me nazari zai so wadatuwar iyalansa. Kalubalen zai kasance matanka da yaranka za su samu kansu cikin kunci da rashin sanin madafa, domin kuwa duk samun mace za ta so tallafin mijinta a gareta. Shawara ga maza wannan hanya ba za ta kai ku ko’ina ba sai tashar da-na-sani, domin inda tunani wadatuwar iyalanku shi ne karin budinku. Ke kuma mace sai ki dage ku nemi sana’a, domin tallafar kanki da yaranki.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos a Jihar Filato:
Batun da ake tattaunawa a wannan mako yana da matukar muhimmanci, musamman domin samun zaman lafiyar iyali. Babu shakka ana samun mazajen da ba sa yarda matan su na aure su san sirrin samun su, saboda fargabar da mazan ke da shi kan cewa, idan matan suka san suna da kudi to, sai sun yi duk yadda za su yi su raba su da wannan kudin, ta hanyar kawo korafe-korafe da matsaloli iri-iri, ta yadda duk abin da suke da shi zai kare. Don haka ake samun wasu da za su boye samunsu ga matan su, sai dai kullum su rika kukan babu. To, a gaskiya wannan ba hali ne mai kyau ba, domin kuwa masu irin wannan hali suna barin iyalinsu cikin kunci, na rashin wadatar kudin cefane, da sauran bukatun gida. Babban abin takaicin ma shi ne idan mutum yana da wadatar amma sai ya gwammaci ya bar iyalinsa cikin kunci, shi kuma ya je waje yana cin mai dadi. Lallai ya kamata mu sake tunani, mu sani fa irin wannan hali ne yake lalata tarbiyyar iyali, har ka ga yara sun fara dauke-dauke, ko bin maza. Allah ya tsare iyalinmu bakidaya daga fadawa cikin wannan jarabawa. Mu kuma Ubangiji Ya wadata mu ta yadda za mu wadata iyalinmu. Mazaje masu iyali mu ji tsoron Allah, mu sani fa cewa, iyalinmu amana ce a garemu, kuma Ubangiji zai yi mana hisabi kan yadda muka kula da su.
Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Naija:
Abin da na fi tunanu suna yin haka ne gudun ka da mace ta yi ta kawo musu bukatunta ne wanda kuma hakkinta ne a wajensu su yi mata su yi wa ‘ya’yansu saboda zamansu take yi, su suka kawo ta suka ajjiye ta. Shawarata bai wuce kana nema dan ‘ya’yanka da matanka da kuma ‘yan’uwanka, ka duba adalci yadda za ka kyautatawa iyayenka da ‘yan’uwanka, ka kyautatawa iyalanka da matanka. Allah ya sa mu dace
Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:
Abu na farko shi ne; rashin adalci, kiyayya, rashin gaskiya, cin amana, wulakanci, fariya. Abu na gaba kuma na kalubalen da za a fuskanta shi ne; yawaitar munanan dabi’u, gurbacewar tarbiyya. Shawara ita ce; Jin tsoron Allah, mata kuma su kama sana’a.
Sunana Princess Fatima Zahra Mazadu:
Gaskiya ya danganta da irin mijin da mace ke tare da shi da yadda asalin suka gina soyayyarsu, shin kan gaskiya da amana ne ko ko kun ginata akan kowa da ra’ayinsa. Mafi akasarin maza tabbas suna boyewa ne saboda rikicin mata, dan wata macen tana ganin kudi a wurin mijinta hankali ya tashi sai an kashesu kafin ta samu sukuni, wani kuma ra’ayin sane kawai da rowa da bakin hali wanda shi kanshi kadai ya sani. Tsantsan rowa ne da kuma rashin yarda, meye rashin yarda? shi ne; ka boye dukiyar ka ga wanda yake mallakinka wanda ba daidai bane, da ita macen za ta yi masa hakan wallahi da duk gari sai an sani cewa ba ta son shi bata yarda da shi ba, da dai sauransu. Rashin daidaito da kuma yarda da juna zai yi karancin. San-samu su zamo daya duk abun da ka samu nata ne, duk abun da ta samu naka ne, wannan shi zai klkara zaman lafiya da kaunar juna da tausayin juna tare da jin kai, kuma kodayaushe daya zai zamo yana yabon dan’uwanshi ta fannin addu’a da kyautatawa.
Sunana Muhammad Isah Zareku Miga Jihar Jigawa:
A gaskiya abun da ya sa maza suke boye samun su ga matan yanzu akwai dalilai da yawa. Kadan daga ciki shi ne; da zarar mace ta san samunka sai su dinga dorawa miji dawainiyar da ba tada wani muhimmanci to, shi ne ya sa maza suke boye samun su. Klubalen da za a fuskanta shi ne da zarar mace ta san samunka ba a fiya zaman lafiya ba, saboda kullum ta rika kawo maka bukatu barkatai da zarar bata samu ba tofa sai ai surutu. Shawarar a nan ita ce miji ya rika sauke duk wani nauyin da Allah ya dora masa, sannan ita kuma matar ta rika saka masa albarka a abun da ya zo da shi, ba tare da tana bibiyar aljihunsa ba.
Sunana Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
So da dama tausayawan da mazajen ke samu wajen matansu kan sa su boye samun su, yanzu mata sun mike da neman kudi kuma abubuwa da dama ba sa jira daga wajen miji saboda tausayawa irin na mace, da wannan damar namiji ke amfani sai ya mike kafa ko ya samu ba zai bayyana ba, saboda yana ganin hana shi za ta yi, idan mace ta fahimci hakan dole zuciyar ta za ta bushe, tausayin mijin zai iya fita daga zuciyarta domin zuciya tana son me kyautata mata ne. Sharawata ga mazaje su daina boye samun su, su san cewa su Allah ya daurawa alhakin ciyar da iyalinsu ba matayen su ba, saboda gujewa irin haka mace tun farko kar ta ma fara daukewa mijinta ciyarwa, har gara sutura da wasu bukatunta, wani abu bayan wannan sai dai ki ba shi, bashi in ya kasa biyan wani sai ki yafe mishi.
Sunana Suwaiba Habeeb daga Gombe:
Su mazan gani suke kamar a kullum idan suna bayyanawa matansu samun su to, za su talautar da su kuma matan sun san suna samu to za su rika tambayar su bukatu daban-daban, wanda hakan kuma hakki ne a kanshi kuma ya kamata ya sauke shi. Shawarata a nan ita ce su mazan su rika yi wa matansu kyakkayawan zato, kuma su rika kokarin sauke hakkin da Allah (SWT) ya daura masu tare da kuma farantawa iyalansu daidai karfinsa.
Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:
Wasu mazan suna da mako ba sa san matan su san suna da kudi, wasu a cewar su wai in kace wa mace kana da kudi mace a lokacin za ta ce muna bukatar abu ka-za da abu ka-za, shi ya sa ba sa fadi amma ai ba uziri bane. Kalubale na farko shi ne; in har matar da ka ke aure ba za ka iya daukar nauyin ta ba shi ne za ka aje ta dauka tunda ba ka iya badawa. Shawara ta ga maza masu irin wanan hali gaskiya ku farga ku gane irin wanan hali ba shi da kyau, Allah ya shige mana gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ma aurata
এছাড়াও পড়ুন:
Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau
Sadau, ya ci gaba da bayyana yadda zai ci gaba rika tunawa da mahaifin nasu, inda ya ce; “Akwai abubuwa da dama da zan rika tuna mahaifina da su, amma abin da zan fi tunawa da shi, wanda kuma zan yi koyi da su shi ne kula da ibada, domin ba za a taba zuwa masallaci ka gan shi a sahu na biyu ba, koda-yaushe a sahun farko za ka gan shi. In dai ibada ce, a gaba za ka gan shi; an shaide shi da haka”, in ji shi.
“Ina godiya ga yan Kannywood da sauran al’ummar da suka halarci jana’iza, wallahi har kwalla na yi saboda irin dandazon jama’a da na gani, Allah ya saka wa kowa da alhairi, sannan kuma ya ba mu hakurin rashin wannan mahaifi namu, muna fatan yadda ya samu kyakkyawar shaida a wajen mutane, ya sa ya samu wannan a can”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp