Baka’i: Za Mu Mayar Da Martani Akan Wasikar Trump Bayan Yin Nazari
Published: 17th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har yanzu, mu ba mu watsa abinda ta kunsa ba.”
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai banbanci a tsakanin yadda Donald Trump yake Magana a fili da kuma abinda wasikar tasa ta kunsa.
Dr. Baka’i ya kuma kara da cewa; Bayan yin nazarin wasikar da abinda ta kunsa za mu bayar da jawabi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kore cewa ziyarar da ministan ma’aikatar tasu Abbas Arakci ya kai zuwa kasar Oman yana da alaka da bayar da jawabin wannan wasikar ta shugaban kasar Amurka.
Da yake mayar da jawabi akan harin da Amurka ta kai wa kasar Yemen, Dr. Baka’i ya ce abin takaici wannan ba shi ne karon farko da Amurkan ta kai wa Yemen hari ba, wanda shakka babu laifi ne kuma abin ayi Allawadai da shi ne.
Dr. Baka’i, ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kasashen musulmi da kungiyar kasashen ta musulmi da su dauki matakin gaggawa akan abinda yake faruwa.
Dangane da barazanar kai wa Iran hari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; Duk wani wuce gona da iri akan Iran zai fuskanci mayar da martani mai tsanani ba tare da taraddudi ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ma aikatar harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Na Maraba Da Karin Abokai Daga Kasa Da Kasa Su Ziyarci Kasar
Guo Jiakun ya bayyana cewa, a ranar 26 ga wannan wata, hukumomin Sin masu ruwa da tsaki sun gabatar da sabbin matakan mayar da kudin haraji ga baki masu yawon bude ido, lamarin da ya kyautata manufar mayar da kudin haraji tun daga lokacin sayayya da kawo sauki ga baki masu sayayya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp