Maduro Ya Jinjina Wa Jagororin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Published: 5th, July 2025 GMT
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro wanda ya bude bikin baje kolin littatafai na kasa da kasa a kasarsa, ya yi jinjina ga Imam Khumaini ( r.a) da kuma jagoran juyi Ayatullah Sayyid Ali Khamnei.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa, A yayin bikin bude taron baje kolin, shugaban kasar na Venezuela ya bayyana girmamawar da yake yi wa jagoran juyin musulunci, tare da yin ishara da ganawarsu a shekarun 2000 da 2010.
Haka nan kuma shugaban kasar ta venezuella ya bayyana yadda ya ga al’adu da ci gaban al’ummar Iran da su ka ja hankalinsa da burge shi matuka.
Bugu da kari shugaba Maduro ya bayyana zurfin hikimar da ya gani a tare da jagoran juyin musulunci, da kuma yadda yake kare tsarin jamhuriyar musulunci da ci gaba da wanzuwarsa a cikin nutsuwa, hakuri, juriya da kuma tsayin daka.
Har ila yau, shugaba Maduro ya yi ishara da yadda Iran take cika alkawalinta a fagen kawancenta da kasarsa Venezuela.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Aragchi Ya Musanta Zargin Da Jamus Take Watsawa Dangane sa Shirin Nukliyar Kasar
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi da zancen ministan harkokin wajen kasar Jamus wanda yake cewa, jinginar da aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA wanda JMI ta yi, ya na nuna cewa ba wanda zai bincika ayyukanta na makamashin nukliya ba, kuma ta rufe kofar tattaunawa Kenan.
Aragchi ya bayyana cewa wannan ba haka bane, saboda shirin nukliyar kasar Iran a halin yanzu ya na karkashin majalisar koli ta tsaron kasar Iran ne, don haka ita ce zata fayyece yadda huldar shirin zai kasance tare da hukumar IAEA. Sannan Iran bata fice daga yarjeniyar NPT ba.
Kasar Jamus dai tana goyon bayan hare=hare da HKI da AMurka suka kaiwa JMI a yakin kwanaki 12, dagan cikin harda hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar. Ya ce aiki ne da bai dace ba wacce JKI ta yi madadin kasashen yamma.