2025-05-23@08:21:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3384

«juyin juya halin Musulunci a»:

    Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji mai girma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) mai girma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaidani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka bude mun kofofin rahamarka.” Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa karshen addu’ar idan za a shiga. Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya. Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli Dakin Ka’aba,...
    Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Umar Iliya Damagun, ya yi Allah Ya isa ga masu zargin da yi wa jam’iyya mai mulki, APC, aiki. Wasu masu ruwa da tsaki a PDP na zargin cewa Damagun da  yi wa jam’iyyar zagon ƙasa APC, shi ya sa yake rura wutar rikicin cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a PDP. Amma a yayin wata hira da ya yi da BBC, Damagun ya yi fatali da zargin, yana mai cewa Allah Zai saka masa tsakaninsa da masu yi masa wannan ƙazafi. “Allah Ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan ƙazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan...
    Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo. Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa...
    Babban Mashawarcin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kashe ’yan ta’adda sama da 13,000 a fadin Najeriya daga lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki a watan Mayun 2023 zuwa yanzu. Ribadu, yayin da yake jawabi a taron Koli na Jam’iyyar APC a zauren taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya bayyana cewa duk da an samu ci-gaba mai sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, yanayin sarƙaƙiyar tsaro ya sa a mafi yawan lokaci jama’a ba sa iya gane waɗannan nasarori nan take. Ribadu ya bayyana cewa an kashe jimillar ’yan tada kayar baya da ’yan fashin daji 13,543, yayin ayyuka daban-daban da sojoji da sauran hukumomin tsaro suka gudanar a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki? Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din. Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka? Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki? Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din. Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka? Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da...
    Kimanin kwanaki biyu ke nan ana jita-jitar cewa sojoji a sun yi nasarar hamɓarar da gwamnatin Shugaba Kasar Kwadebuwa, Alassane Ouattara. Jita-jitar ta fara yaɗuwa ne tun bayan jin ƙarar harbe-harbe a yankunan ƙasar da dama musamman a babban birnin ƙasar na Abijan. Ba mu tilasta wa kowa ya koma APC ba — Tinubu Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri Wasu rahotanni na nuna cewa an samu ɓarkewar rikici ne a cikin birnin na Abijan, lamarin da ake hasashen ya yi sanadiyar masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Ouattara kimanin mutum 33 cikin kwana biyu. Sai dai har ya zuwa yanzu babu wani tabbataccen rahoton daga majiya mai ƙarfi da ke bayyana hakikanin abin da ke...
    Wasu masana a tarayyar Najeriya sun jinjinawa yadda Najeriya da Sin suka daga dangantakarsu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni a bara, matakin da ya tabbatar da goyon bayansu ga kokarin tinkarar kalubalen karin harajin kwastam da Amurka ke dora musu bisa radin kai. Kwanan baya, an gudanar da taron tattaunawa kan yadda za a tinkari harajin kwastam da Amurka ke kakabawa sauran kasashe a birnin Abuja hedkwatar Najeriya, inda babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Najeriya bisa dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, da shawarar “ziri daya da hanya daya” da dai sauransu, ba ingiza bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a Afirka kadai...
    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki masu cewa gwamnatinsa na ingiza ’yan Najeriya wajen bin tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa ba za ka iya zargi mutane kan zaɓar jam’iyya ba. Da yake jawabi a wajen taron ƙoli na jam’iyyar APC  karo na farko da aka yi a ranar Alhamis, da ya gudana a fadar shugaban ƙasa a Abuja, shugaban ya ce “jam’iyya ɗaya ce ke mulki”. Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe  “Ga waɗanda har yanzu suke tunanin fita daga jam’iyyarsu, ƙasar nan taku ce, ku riƙe ta, ga masu maganar tsarin jam’iyya ɗaya, jam’iyya ɗaya ce ke...
    Modric, ya lashe kofuna 28 da suka hada da gasar zakarun Turai 6 da Laliga 4 tun lokacin da ya koma Real daga Tottenham a shekarar 2012.   “Na zo ne a shekarar 2012 tare da fatan sanya rigar yan wasan da suka fi fice a duniya da kuma burin samun manyan nasarori, Real Madrid ta canza rayuwata a matsayina na dan wasan kwallon kafa da kuma mutum, ina alfahari da kasancewata a daya daga cikin mafi kyawun kulob a tarihi” inji shi.   Real za ta bude gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa da Al-Hilal ta Saudi Arabiya a ranar 18 ga watan Yuni, sannan kuma za ta kara da Pachuca ta Mexico da RB Salzburg ta...
    A gun taro karo na 28 na kwamitin madatsar ruwa na duniya da ake gudanarwa, an bayyana cewa kasar Sin ta cimma nasarar gina madatsun ruwa masu kunshe da fasahar zamani da dama, kuma ci gaban da take samu a bangaren kirkire-kirkire, da nasarorin da take samu a fannin gudanar da harkoki masu masaba da hakan na jawo hankalin kasa da kasa. Ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta kyautata aikin na’urorin sa ido kan kananan madatsun ruwanta dubu 51, da zummar kafa tsarin taurarin dan Adam, da jiragen sama marasa matuka, da na’urar rada, da tasoshin doron kasa, da na’urorin karkashin ruwa, da na’urorin sa ido bai daya. Ban da wannan kuma, Sin ta fara aikin gwaji a wurare...
    Arewa Tech Fest, taron koli ne na fasaha da kirkire-kirkire na kwanaki uku, wanda ke tattaro ’yan kasuwa, kwararru masu fasaha, masu zuba jari, da masu tsara manufofi don bunkasa fasahar kere-kere a Arewacin Nijeriya. El-Rufai ne da kansa ya shirya bikin.   Minista Tijani, wanda ya gabatar da jawabi mai mahimmanci, ya yi magana a kan sauye-sauye na zamani da kirkire-kirkire a sassan gwamnati da masu zaman kansu na Nijeriya.   El-Rufai ya isa wurin taron ne a makare, inda ya nemi afuwar mahalarta taron tare da bayyana cewa ya samu jinkiri saboda wani muhimmin taron siyasa da aka gudanar a yammacin jiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Ko shakka babu, ba wani tsari ko salon ciyar da al’umma gaba da za a iya cewa zai dace dari-bisa-dari da dukkanin sassan duniya bai daya, amma duk da haka, daukacin kasashen duniya za su iya koyi daga kwarewar kasar Sin, da tsawon lokacin da ta shafe tana gwada dabarunta na ci gaba wadanda suka haifar da da mai ido. Yayin da a nasu bangare sassan kasa da kasa ke da damar tsara manufofi daidai da burikansu da yanayin da suke ciki. Wasu masharhanta na ganin kwarewar da Sin ke samarwa duniya, tamkar sabon zabi ne ga sassa masu fatan gwada wani salo na bunkasa kasashe masu tasowa, wanda ya sabawa na yammacin duniya, don haka sassa daban daban ke...
    Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe  An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
    Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe  An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
    Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa.   “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida. Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan  su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39. Sanarwar ta MDD ta ci gaba...
    Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar. Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar. Haka nan kuma cibiyar za ta kyautata ayyukanta ta hanyar harba taurarin dan’adam a sararin samaniya da kafa cibiyoyin bibiyar yanayi domin yin musayarsu da kasashen nahiyar da kuma wajenta.
    Jaridar ‘yan sahayoniya ta “Ma’ariv’ ta buga labarin da yake cewa; Isra’ila tana fuskantar matsalar diplomasiyya saboda ci gaba da yakin Gaza. Jaridar ta kuma ce; A halin yanzu “Isra’ila” tana fuskantar abinda ta kira “Tsunami Na Diplomasiyya” saboda yakin da take ci gaba da yi a Gaza. Haka nan kuma jaridar ta soki gwamnatin Netanyahu tare da bayyana ministan harkokin waje Gadion Sa’ir wanda ta ce, ba abinda ya dame shi kamar ci gaba da zama akan kujerarsa, da cewa; Ba ya fahimtar girman musifar da take tunkaro Isra’ila.”  Har ila yau, jaridar ta yi suka ga ministar sufuri Miri Rigiv da cewa saboda ta’annuti, ta ki yin furuci da cewa Isra’ila tana karkashin takunkumin zirga-zirga ta sama, kuma...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci Sin da Faransa su kasance karfi abun dogaro wajen tabbatar da odar duniya da inganta ci gaban duniya da jagorantar hadin kai tsakanin kasa da kasa. Da yake zantawa ta wayar tarho da shugaba Emmanuel Macron a yau Alhamis, Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Faransa da su hada hannu wajen kare matsayi da ikon MDD da kare ka’idojin cinikayya na duniya da odar duniya da kuma tabbatar da cudanyar bangarori daban daban. Ya kara da cewa, kasar Sin tana daukar Turai a matsayin mai zaman kanta a duniyar dake da kasashe daban daban masu karfi. Ya ce, Sin na goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta karfafa cin gashin kanta...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta sanar da samun nasarar kuɓutar da wata mace mai shekara 22 da aka yi garkuwa da ita tare da kama wasu mutum biyu. An kama mutum biyun ne da ake zargi da alaƙa da wani mummunan hari a ƙauyen Tashan Randa da ke ƙaramar hukumar Fika. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce samamen da aka gudanar tare da haɗin gwiwar mafarautan yankin, ya nuna wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da rundunar take yi na yaƙi da rashin tsaro a jihar. An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Dangote ya sake rage farashin man fetur Sanarwar...
    Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mai suna Mohammed Umar mai shekara 19, mazaunin wata unguwa da ake kira hanyar Abuja a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu bisa laifin sanya tufafi da shigar mata. Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Ngoruje, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa, mutumin yana ta kai-kawo a cikin harabar cocin Ngurore Lutheran Church of Christ Nigeria. Dangote ya sake rage farashin man fetur An yi Jana’izar Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a Zariya “Kamen matashi ya biyo bayan rahoton da wani mazaunin garin (da aka sakaya sunansa) ya kai hedikwatar ’yan sanda ta Ngurore, bayan ya lura da sintirin wanda ake zargin a cikin harabar...
    “Hukumar ta amince da ƙirƙiro sashen AI a ƙarƙashin ɓangaren fasahar sadarwa na hukumar domin cin ribar AI da fasahar da take ɗauke da ita da kuma magance ɓarnar da fasahar ka iya kawowa a lokutan zaɓe” a cewar sanarwar   Wannan matakin da INEC ta ɗauka dai ya biyo bayan tarurruka da dama da ma’aikatan hukumar suka halarta a sassa daban-daban na duniya a kan AI inda ƙasashen Afirka da dama suka tattauna domin rungumar sabuwar basirar ta hanyar yin amfani da ita a inda ya dace da kuma maganin yin amfani da ita wajen kawo cikas a zaɓe musamman yaɗa labarun ƙarya a lokutan zaɓe da sauransu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Kamfanin Dangote wanda ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sake sabon ragin farashin man fetur na N15 a gidajen da ke hulɗa da shi. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce a sakamakon wannan ragi, ‘yan Najeriya za su sayi man fetur a kan farashi kamar haka: Naira 875 kowace lita a Legas; Za a sayar Naira 885 kowace lita a yankin Kudu maso Yamma; A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya za a sayar kan Naira 895 kowace lita; yayin da za a sayar da shi kan Naira 905 kan kowace lita a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, da Arewa maso Gabas. Waɗannan farashin za su yi aiki ne...
    A jawabinsa yayin Kaddamar rabon kayan Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya bayyana cewa “Komawar mu jam’iyyar APC ya nufin kawar da adawa don samar da ci gaba a jihar Kebbi, kuma zamu yi hadin gwiwa da gwamnatin, Gwamna Nasir Idris don amfanin mutanenmu ga irin ayyukan da ya gudanar a dukkan kananan hukumomin 21 na jihar, Wanda shi ne muke kira a ko da yaushe cewa a samar da cigaba ga jama’ar da muke shugabanta,” Inji Sanata Muhammadu Adamu Aliero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
      Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025. Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu a fannin gine-ginen ababen more rayuwa, musamman hanyoyi, karkashin shirin Renewed Hope Action Plan na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Daya daga cikin manyan nasarorin da rahoton ya nuna shi ne ci gaba da aiwatar da shirin Highway Development and Management Initiative (HDMI), wanda ke amfani da tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP). Wannan tsarin ya ba da damar janyo hannun jari...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An gudanar da Jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna. Marigayin dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da aikace aikacen sa a masana’antar Kannywood da Nollywood. Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun yace Umar ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Asibitin Koyarwa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya. Yace rasuwar ya faru ne a daren ranar laraba sailin da akayi Jana’izar sa a ranar Alhamis a makabarta dake Zariya. Shi dai Marigayin har ilau malami ne a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zariya. Ya rasu ya bar yan uwanshi da dama Hoton...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda alaka da Iran za ta iya taimakawa al’ummar Siriya, a shirye mahukuntan Iran su amsa bukatar ta.” A wata hira da tashar talabijin ta Al Sharq, Araqchi ya jaddada dimbin damammaki, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi wajen kulla kyakkyawar huldar makwabtaka da yankin da ke kewaye, kuma Iran ta bi ta wannan hanya.” Ya kara da cewa: “Iran ta...
    Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata. An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai. A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika...
    Ya kuma ce suna sane da cewa yajin aikin zai iya shafar jama’a musamman a Katsina. “Ba ma’aikata kaɗai muke ba – iyaye ne mu kuma masu ciyar da iyali. Abin da muke nema kawai haƙƙinmu ne,” in ji shi. Yajin aikin zai iya haifar da tsaiko wajen samun wutar lantarki a yankin, musamman a Katsina inda yajin aikin ke da zafi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni.   Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban Kamfanin na CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya jaddada bukatar sauya ra’ayi game da lamuni, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauke shi a matsayin wani makami na bunkasa maimakon akasin haka.   “CREDICORP, wacce aka kafa a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wata cibiya ce ta kasa da ke aiki don tabbatar da dimokaradiyya ta hanyar samun lamuni ga duk ‘yan...
    Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Sanata Muhammad Adamu Aleiro, ya raba wa al’ummar mazabar sa kayan tallafi da nufin ba su damar dogaro da kai.   Kayayyakin sun hada da babura 150 (Keke NAPEP), babura 114, firiza mai zafin rana guda 302, injin nika 750, famfunan ruwa mai amfani da hasken rana 500, injin dinki 800 da kuma buhunan taki 3,400.   Da yake jawabi a wajen bikin raba kayayyakin a karamar hukumar Aleiro ta jihar Kebbi, Sanata Adamu Aleiro, ya ce hakan na daga cikin romon dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa kadai, har ma da jihar.   Sanata Aleiro, ya lissafo wasu ayyukan da ya aiwatar a matsayin aikin mazabu a kananan hukumomi takwas na mazabarsa da suka hada...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa jarirai dubu 14 a Gaza kan iya rasa rayukansu muddin Irsa’ila ta ci gaba da killace Zirin da hana shigar da kayan agaji. Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher na maida martini ne kan matakin gwmanatin Isra’ila na kyale manyan motoci hudu na agaji su shiga Gaza inda ya ce wannan tamkar”digo ne a cikin teku.” “Akwai jarirai 14,000 da za su mutu a cikin sa’o’i masu zuwa idan ba za mu iya kaiwa gare su ba inji shi. Ya ce motocin agajin da ke dauke da kayan abinci na jarirai da abinci mai gina jiki, suna cikin Gaza amma ba su kai ga farar hula ba saboda gwamnatin Isra’ila...
    Masana sun yi kira ga hukumomi da su yi bincike mai zurfi don gano waɗanda ke taimaka wa Boko Haram sannan a hukunta su domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama.   Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye.   Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622,...
    Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.”   Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.”   Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
    A bangaren masaku ma, masakar Zhejiang Yingfeng ta samu bunkasar ayyukanta musamman wajen rage yawan abubuwan da ba a bukata domin fitar da kayan da ake sarrafawa da tsafta, bayan ta rungumi amfani da fasahar zamani. Haka nan bangaren rina kaya ya samu ci gaba da kusan kashi 80 zuwa 95 cikin dari. Bangaren aikin gona shi ma yana samun habaka bisa amfani da fasahohin zamani wajen ayyukan noma, da kula da gonaki, da sayar da amfanin gona da sauransu. A garin Zhangzhuang dake gundumar Shangshui ta birnin Zhoukou dake lardin Henan na tsakiyar kasar Sin, ana iya ganin yadda ake amfani da na’urori da fasahohin zamani a ayyukan gona a bangaren zuba taki da ban-ruwa, da taraktocin noma da...
    A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama.   Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye.   Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622,...
    Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.”   Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.”   Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki zamantakewa ysaro da sauransu, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe kuma mu ji ra’ayin masana dangane da su. Dafatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da tattaunawa    tsakanin JMI da kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Wanda ya zuwa yanzu an gudanar zagaye na 4 na tattaunawar. Har zuwa wannan lokacin dai dukkan bangarorin suna fadar cewa ana samun ci gaba a tattaunawar. Amma bayan kwanaki da        ...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta soki yunkurin da Amurka ke yi na hana kasashen duniya amfani da sashen harhada na’urorin laturoni na Chips kirar kasar Sin. Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, ta kira yunkurin na Amurka da cin zali daga bangare guda, da baiwa kasuwa kariya, matakin da tabbas zai illata tsarin ayyukan masana’antun kira da rarraba sassan semiconductor na duniya.   Kazalika, kakakin ma’aikatar ya ce a baya bayan nan sashen lura da harkokin cinikayya na Amurka ya fitar da wasu bayanai, ta fakewa da batun wai ana keta dokokin Amurka na fitar da hajoji, da nufin haramtawa sassan kasa da kasa amfani da sassan na’urorin Chips masu kunshe da manyan fasahohin sarrafa bayanai...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 3 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan shari’ar BBC da mawaƙi Abdul Kamal. Tunda farko Abdul, ya maka kafar ne a kotu, inda yake neman ta biya shi diyyar Naira miliyan 120, kan zargin amfani da waƙarsa a shirinsu na “Daga bakin mai ita” ba tare da izininsa ba. Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum A zaman shari’ar na ranar Litinin, lauyan mai ƙara, Barista Bashir Ibrahim Umar, ya gabatar da makaɗin waƙar, Muhammad Sani Uba a matsayin ɗaya daga cikin shaidun wanda ke ƙara. Makaɗin ya tabbatar wa kotu cewa shi ne,...
    Sojojin HKI sun bude wuta nag aske kan jami’an diblomasiyya na wasu kasashen Turai wadanda suke kokarin shiga sansanin yan gudun hijira na Jenin don galin yadda rayuwa take tafiya a cikinsa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jamilan diblomasiyya wadanda suke ziyarar sansanin yan gudun hijiran a yau Laraba dai sun hada da jakadun kasashen  Austria, Brazil, Bulgaria, Canada, Chile, China, Masar, Faransa, India, Japan, Jordan, Lithuania, Mexico Morocco, Poland, Portugal, Romania, Rasha, Sri Lanka, Spain, Turkey, tarayyar Turai (EU), da kuma Burtaniya.  Tare da su akwai wakilai daga wasu kasashen duniya da kuma yan jarida. Ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin Falasdinawa ne ta shiryawa wadannan kasashen ziyara zuwa wannan yankin na yamma da kogin Jordan don...
    Kwamiti mai kula da al-amuran harkokin waje a kasar Burtaniya tana matsawa sakataren harkokin wajen kasar David Lammy kan cewa ya amince da kasar Falasdinu mai zaman Kanata. Jaridar Telegram ta kasar Burtaniya ta nakalto wannan rahoton a yau Laraba, ta kuma kara da cewa Dan majalisa Emily Thomberrry ya kara da cewa wannan mataki na farko ne, idan Lammy ya bada wannan sanarwan a cikin wata mai zuwa a lokacin haduwarsa da Saudiya da Faransa a wani babban taro wanda zai bada damar daukar matakai nag aba. Jaridar tace, wannan maganar tana zuwa ne bayan da sakataren ya dakatar da tattaunawa ta harkokin kasuwanci da HKI, da kuma kiran jakadan HKI a London don gabatar da korafinsa kan sake...
    Zanga-zangar ta haifar da cunkoso a kan hanyar yayin da matafiya da suka hada da manyan motoci a kan titin suka tsaya cak na tsawon sa’o’i.   Matasan sun kuma koka da yadda har yanzu ba a sako wani jigo a jam’iyyar LP ba, Okasime Olowojoba da aka yi garkuwa da shi kusan wata guda duk da biyan sama da Naira miliyan 5 kudin fansa.   Daya daga cikin masu zanga-zangar Paul Lawani ya ce, “Ba za mu iya ci gaba da zama bayi a kasarmu ba, ya kamata gwamnati ta fada mana abin da take yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya (NUEE) reshen Jihar Kano, ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani saboda rashin biyan haƙƙoƙinsu da kamfanin KEDCO ke yi. Sakataren tsare-tsaren ƙungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Muhammad Babangida ne, ya bayyana hakan a wani saƙon murya da Freedom Radio ta wallafa. Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu” A cewarsa, ma’aikatan KEDCO sun shafe sama da watanni 100 ana cire musu kuɗin fansho daga albashinsu, amma ba a tura kuɗin zuwa inda ya dace ba. “Tun bayan kafa KEDCO aka fara cire wa ma’aikata kuɗin fansho, amma har zuwa yanzu ba a tura su inda ya...
    Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi ikirarin cewa akwai mutanen da ke aiki a matsayin ‘yan leken asiri ga ‘yan ta’adda da suka hada da Sojoji, ‘yan siyasa da sauran mutanen gari. Da yake jawabi yayin hira da kamfanin labarai na ‘News Central’ a ranar Laraba, gwamnan ya jaddada bukatar sabunta dabarun leken asiri da daukar kwararan matakai don magance matsalar rashin tsaro a yankin. Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna “Akwai wadanda suka yi hadin gwiwa da ‘yan ta’adda daga cikin sojojin Nijeriya, cikin ‘yan siyasa, da kuma cikin mazauna yankunanmu, abin da za mu yi shi ne mu karfafa fasahar leken...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa wasu daga cikin sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su bayanai. A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda. Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON Gwamnati za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta ƙwato a hannun Emefiele  Ya ce: “Akwai masu bai wa Boko Haram bayanaj a cikin sojoji, ’yan siyasa da sauran jama’a. Za mu ƙarfafa leƙen asiri, kuma mu ɗauki tsattsauran mataki a kansu.” Gwamna Zulum ya ce dole...
    “An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.   “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.   “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.   “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...
    “An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.   “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.   “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.   “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa ta yi jigilar maniyyatan Najeriya 32,549 zuwa Saudiyya don gudanar da Hajjin shekarar 2025. Wannan adadi ya kai kashi 79.1 na jimillar waɗanda ake sa ran za su yi Hajji daga Najeriya. DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu” Mun dakatar da sanya tallan magungunan gargajiya a fina-finai – Abba Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce an kammala jigilar ne ta hanyar amfani da jirage 79 tun daga ranar 9 ga watan Mayu, 2025. Rahoton Aminiya ya nuna cewa kimanin maniyyata 42,000 ne ake sa ran za su halarci Hajjin bana daga Najeriya. Jihohi da dama kamar Adamawa da Filato sun kammala jigilar maniyyatansu...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu nay au zai yi Magana dangabe da “Tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran da Amurka yana tanga-tanga’ wanda ni tahir amin zan karanta. Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa, da alamun tattaunawa tsakanin kasar ta kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran ba zai je ko in aba, saboda yadda bangaren Amurka a cikin kafafen yada labaransu, daga ciki har da jakadan Amurka kan al-amuran gabas ta tsakiya, kuma shugaban tawagar Amurka a tattaunawar wato Steve Witkoff  ya fito a kafafen yada labarai na Amurka yana fadar cewa duk wata yarjeniyar da za’a cimma da kasar Iran nan gaba dole sai...
    Kungiyar Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting CP, Viktor Gyokeres kamar yadda jaridar wasanni ta football365 ta ruwaito. Arsenal ta fuskanci matsalolin ‘ƴan wasan gaba a kakar wasan da ke dab da ƙarewa, yayin da ƙungiyar ta gaza lashe kowane irin kofi. Bayan ƙarewa a mataki na biyu a Gasar Premier da samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai ta baɗi, a yanzu hankalin ƙungiyar ya karkata kan samun ɗan wasan gaba, domin sake gina kanta. A ƙarshen kakar wasa da muke ciki ne Gyokeres ɗan asalin Sweden zai bar ƙungiyar Sporting bayan ƙarewar kwantiraginsa, kamar yadda Fabrizio Romano fitaccen ɗan jaridar wasanni ya bayyana a shafinsa na X. BBC
    Jihar Jigawa da Babban Birnin Tarayya su ma za su kammala nasu a yau. Jihar Kwara na da sauran mahajjata 137 kuma za su tashi a jirgin Max Air a Kano da rana. Mahajjatan daga Jihar Binuwai za su haɗe da waɗanda ke yankin Kudu maso Kudu domin tafiya tare a jirgi guda da zai tashi a ranar 23 ga watan Mayu, wanda zai zama jirgi na ƙarshe daga wannan yanki. A cewar Fatima Sanda Usara, Babbar Daraktar Watsa Labarai a NAHCON, ba a soke jirgi ko ɗaya ba tun lda aka fara jigilar maniyyatan. NAHCON ta gode wa mahajjata da al’ummar Nijeriya baki ɗaya bisa haƙuri, addu’o’i da goyon baya, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ba su tunanin cewa tattaunawar Iran da Amurka za ta haifar da kyakkyawan sakamako Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Iran ba ta jiran izinin kowa wajen inganta sinadarin Uranium, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da manufofinta. Jagoran ya ce ba su yarda cewa tattaunawar za ta kai ga cimma nasara ba. A jiya Talata ne aka gudanar da biki a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) na tunawa da shahadar marigayi shugaban kasa Ayatullah Ibrahim Raisi da mukarrabansa. Bikin ya samu halartar Jagoran juyin juya halin Musulunci, da shugabannin bangarori uku na gwamnati, da manyan jami’ai, da taron iyalan shahidai, da kuma bangarori daban-daban na al’umma....
    Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kalamai masu karo da juna na Trump da mataimakansa sun zubar da kwarin gwiwa ga gwamnatin Amurka Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya bayyana cewa: Sabani da ake ci gaba da yi a cikin maganganu da ayyukan Trump da takwarorinsa na haifar da rashin amincewa da gaskiyar gwamnatin Amurka. Ali Akbar Velayati mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi tsokaci a cikin wani sako da ya wallafa a dandalin X kan kalamai masu cin karo da juna da jami’an Amurka suka yi. Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya ce ci gaba da cin karo da juna...
    Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwaryar Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makonni Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwarya a Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makwanni, lamarin da zai sa kasar ta fada cikin yakin basasa matukar Amurka ba ta ba ta hadin kai ba. A yayin zaman Majalisar Dattijan Amurka, Sakataren harkokin wajen kasar Rubio ya yi furuci da cewa: Idan Amurka ta yi aiki da gwamnatin Siriya, yana iya yiwuwa, gwamnatin ta samu nasara, ko kuma gwamnatin ta kasa samun nasara idan Amureka ba yi aiki da ita ba, kuma tabbas ba zata taba samu nasara ba. Ya kara da cewa: “A hasashen Amurka, idan aka yi...
    Sanatocin jihar Kebbi guda uku da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, sun bukaci hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar domin samun nasara a zaben 2027. Sanata Adamu Aliero, wanda ya yi jawabi a madadin sauran sanatocin, ya bayyana haka a wani taron jiga-jigan jam’iyyar APC da reshen jihar ya shirya a Birnin Kebbi. Sanata Aliero ya ce sauya shekar su daga jam’iyyar adawa PDP zuwa jam’iyya mai mulki APC, domin cigaban jihar ne gaba ɗaya. A cewarsa, akwai ayyuka da dama da za a aiwatar a jihar Kebbi, amma saboda wakilan jihar a majalisa suna jam’iyyar adawa, aka hana jihar damar cin gajiyar wadannan ayyukan. Game...
    A baya-bayan nan, Bankin Duniya ya ce tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙaru da kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2024, alamar cewa tattalin arziƙin na farfaɗowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A bana ake cika shekaru 80 da kawo karshen yakin duniya na II da ma dawowar yankin Taiwan karkashin ikon babban yankin kasar Sin, wadda nasara ce da babu wanda zai goyi bayan lalata ta, sai masu neman cimma wani buri na kansu. La’akari da shekarun da aka shafe, da tsayawar kasar Sin tsayin daka kan tabbatar da iko kan yankunanta, ya kamata yankin Taiwan da masu tunzura shi su fahimci cewa, suna bata lokacinsu domin manufar kasar Sin daya tak, manufa ce da ta samu amincewar kasa da kasa kuma babu wanda zai iya sauyata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dangantaka na ƙara rincaɓewa tsakanin masu shirya finafinai Kannywood da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, wacce daya daga cikin jaruman fina-finan Kannywood Abba El-Mustapha, ke jagoranta. A baya-bayan nan, hukumar ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22, bayan saɓaninta da wasu masu shirya fina-finai, inda take zargin cewa fina-finansu sun ƙetare iyaka. Sai dai masu shirya fina-finan sun bayyana cewa sam hukumar ba ta da hurumin dakatar da waɗannan finafinai. NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kula Da Lafiyar Jikinku DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan rigimar da ta balle tsakanin hukumar da masu shirya finafinai masu dogon...
    Birtaniya ta dakatar da tattaunawar cinikayya cikin ‘yanci da Isra’ila, bayan firaminista Keir Starmer ya ce ya kadu da yadda Isra’ila ke ci gaba da yakin Gaza. Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ya bayyana matakin jingine batun ciniki tsakanin Birtaniya da Isra’ila, ya kuma nemi jakadan Isra’ila a Birtaniya ya bayyana a gaban Ofishin Lamurran Cikin Gidan kasar domin ya amsa tambayoyi game da yakin da kasarsa ke ci gaba da yi a Gaza. Mista Lammy ya ce ministan da ke lura da lamurran da suka shafi gabas ta tsakiya na Birtaniya, Hamish Falconer, zai sanar da Hotovely cewa, “hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza har na tsawo makonni 11 mugunta ce kuma babu hujjar yin hakan” ....
    Bayan sanarwar ba-zata da Amurka ta yi a makon da ya gabata, Tarayyar Turai ta ce za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria. Ministocin harkokin waje da ke taro a Brussels ne suka yanke shawarar dage dukkan takunkumin tattalin arzikin kan Siriya. “Muna son taimakawa al’ummar Siriya wajen sake gina sabuwar Siriya,” in ji jami’ar kula da harkokin wajen Tarayyar Turai Kaja Kalas. Tarayyar Turai ta kuma yi alkawarin bayar da Yuro biliyan biyu da rabi domin sake gina kasar. Matakin dage wannan takunkumin da aka kakabawa gwamnatin Bashar al-Assad tun daga shekara ta 2011, zai bada damar sakin kadarorin kasar da har yanzu ke daskare, sannan kuma zai baiwa hukumomin kasar damar neman zuba jarin da suke...
    Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin tsaro a kafatanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar   Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Mohammad Bello Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a taron shirye-shiryen babban taron tsaro da za a gudanar a Minna.   Janar Mohammad Bello Abdullahi ya kara da cewa Gwamnati jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da rashin tsaro, inda ya bukaci hadin gwiwa daga kowane bangare domin cimma burin da aka sanya a gaba.   A cewarsa, babban taron zaman lafiya da tsaro na farko da za...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse. Ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen siyan motoci Sharon guda goma sha shida da kuma motoci Golf Volkswagen guda ashirin domin raba wa mambobin ƙungiyar guda talatin da shida a matsayin tallafin dogaro da kai. Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma yanke shawarar fitar da...
    A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na kasar Sin masu daraja. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta sanar da dakatar da duk wani nau’in tallan magungunan gargajiya a cikin fina-finai, a kan titi ko amfani da lasifika. Wannan na cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, wadda Jami’in Yaɗa Labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya raba wa manema labarai. ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Shugaban hukumar ya ce wannan matakin na da nufin kare martabar masana’antar fina-finai da kuma tabbatar da cewa duk wani bayani da ke zuwa ga jama’a ya bi ƙa’idoji da doka. “Yawancin tallace-tallacen maganin gargajiya da ake...
    Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu, 2025. ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Rahotanni sun nuna cewar a ranar Laraba za a fara bidirin bikin har zuwa ranar Asabar. An shirya gudanar da walima, ƙwallon ƙafa, saukar karatun Alƙur’ani da sauransu har zuwa ranar ɗaurin aure. A yanzu matashiyar ta fi mayar da hankali...
    Da safiyar yau Talata mazauna yankin “al-Daraj’dake Gaza su ka  farka daga cikin sanadiyyar  harin da jiragen yakin HKI su ka kai wa makarantar ” Musa Bin Nusair” dake karkashin hukumar agaji ta UNRWA” wacce take kunshe da daruruwan ‘yan hijira. Dama dai wannan ba shi ne karon farko da wannan yankin yake fuskantar hare-hare daga HKI ba. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Harin na yau ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 44,mafi yawancinsu mata ne da kananan yara, baya ga wani adadi mai yawa na Falasdinawan da su ka jikkata. Kananan yara da suke rayuwa a cikin wannan sansanin ‘yan hijira sun rika kai da komowa suna neman kayan wasanninsu daga karkashin baraguzai. A kusa da...
        Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami tare da ƙwato motocin sata guda huɗu, bayan wani samame da suka kai. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu nasarar ne a ranar 10 ga watan Mayu, 2025, inda tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin CSP Rabiu Gidado ta kama wani da ake zargi, Saidu Abubakar, a Jihar Filato. Malamai sun gindaya sharaɗi kafin janye yajin aiki a Abuja  An kama ɗan bindiga a hanyar zuwa aikin Hajji a Sakkwato An same shi da wata mota ƙirar Toyota Corolla samfurin 2016 da aka sace wa wani mazaunin unguwar Naibawa a Kano. Yayin gudanar da bincike, Abubakar ya amsa cewa...
    A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa, rage talauci wanda batu ne da ya shafi duniya baki daya, buri ne na daukacin kasashen duniya. Ya ce duk da cewa aiki ne mai matukar wahala, amma duk da haka kasar Sin ta cimma nasarar rage shi daidai da ajandar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030, shekaru 10 gabanin wa’adin karshe na ajandar. Hakan ya shaida ingancin...
    Malaman makarantu da ma’aikatan ƙananan hukumomi a Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun bayyana cewa ba za su janye yajin aikin da suka shiga ba, har sai an biya malaman firamare bashin albashin da suke bi. Yajin aikin ƙarƙashin jagorancin rassan ƙungiyar malamai ta ƙasa (NUT) da ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), da na Abuja. Zulum zai saya wa sojoji da ’yan sa-kai ƙarin motoci don yaƙar Boko Haram An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin maniyyata a Saudiyya Wani mamba a ƙungiyar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana wannan matsaya ne a yayin wasu taruka guda biyu da suka gudanar a ranar...
    Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya.   Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa.   “Ya kasance mutum mai dattako wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da cigaba,” in ji gwamna Bala.   Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi, iyalai da al’ummar jihar da fatan Allah ba su haƙurin juriya na wannan babban rashin.. ...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Ya ce za a bai wa ’yan sa-kai motoci shida ƙirar Toyota Hilux, ciki har da CJTF, mafarauta da ’yan banga, sannan za a bai wa sojoji ƙarin motoci huɗu masu bindiga. Zulum, ya kuma raba wa iyalai 10,000 da ke fama da talauci a yankin kayan abinci, yawancin waɗanda...
    A ganin mista Akanbi, manufofin kasashen yamma ne dalilin da ya haifar da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashe dake nahiyar Afirka. Misali, kamfanonin kasashen yamma sun samu damar mamaye bangaren hakar ma’adinai na Najeriya, kana sun takaitawa kasar damar sarrafa ma’adinai, da ta raya masana’antu. Ban da haka, matsayin musamman na dalar Amurka a fannin ciniki, da yadda ake sarrafa farashin kudin, sun tsananta yanayin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, da jefa kamfanonin kasar cikin mawuyacin hali. Ta yaya za a iya daidaita matsalolin da ake fuskanta? Mista Akanbi ya ba da shawarar daina dogaro da kasashen yamma, da tabbatar da bangarorin tattalin arzikin kasa da za a ba muhimmanci, bisa ra’ayin kasar, kamar yadda kasar...
    Wasu makiyaya biyu sun rasu bayan da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe musu wuta a kusa da ƙauyen Tahore, da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da mamatan ke dawowa daga kasuwar Maikatako a kan babur. Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Harin ’yan bindiga ya sa Zamfarawa sun koma kwana a jeji Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana sunan mamatan a matsayin Umar Sa’idu da Rashida Yakubu. Ya ce lamarin ya faru ne da yamma, kuma ya sanar da manyan jami’an tsaro ciki...
    Mahajjata da jami’ai sun yaba da wannan gaskiya da rikon amana. Wasu sun ce hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa ga tsaron mahajjata da amincin tsarin aikin hajji. “Alhamdulillah, Hajiya ta samu kuɗinta gaba ɗaya,” in ji wani jami’in sansanin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan haka, ‘yansanda sun hanzarta daƙile harin, inda suka kama su a ranar 15 ga watan Mayu, 2025. Da ‘yan fashin suka hango ‘yansanda, sai suka fara harbi. A lokacin musayar wutar ne, Babanle ya mutu. ‘Yansanda sun kama sauran tawagar ƙungiyar guda bakwai a wajen. Wasu daga cikinsu tsoffin fursunoni ne, yayin da ɗaya daga cikinsu fursuna ne da ya tsere daga gidan yari. Hakazalika, ‘yansanda sun ƙwato wasu kayayyaki ciki har da mota ƙirar Toyota Camry, babur ƙirar boxer, harsasai, bindigogi ƙirar AK-47 da kuma wata bindiga ƙirar gida. SP Adeh, ta ƙara da cewa shugaban ƙungiyar, Solomon Bawa wanda aka fi sani da Fasto Mogu, ya tsere tare da wani mutum bayan sun samu rauni. Ta roƙi...
    ’Yan sanda sun bindiga wani wanda ake zargin dan fashi ne har lahira, sa’annan suka kwato bindigogi bakwai a unguwar Maitama da Abuja. Kwamishinn ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Ajoa Adewale, ya sanar a safiyar Talata, cewa rundunar ta kama gungun wasu mutum bakwai da suka kware wajen aikata fashi d makami da kuma kwcen motoci. Ajao ya ce ’yan fashin suna ganin ’yan sanda suka bude musu wuta, inda jami’an suka yi nasarar harbe wani wanda aka fi sani da Baballe, har lahira, suka kama wasu guda bakwai. Shugaban ’yan fashin, wanda ake kira Pastor Mogu da wani mutum daya sun tsere da raunin harbi a jikinsu. Abubuwan da aka kwace a hannun ’yan fashin sun hada da bindigogi...
    Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen matan da aka kama ba, amma jami’an leƙen asirin Nijeriya sun ce matan na da muhimmanci wajen binciken hanyoyin samun kuɗaɗe da tallafin da ‘yan ta’adda ke samu. Wani masani kan yaƙi da ta’addanci ya ce wannan ci gaba ya ƙara bayyana yadda matsalar tsaro a Nijeriya ta fara ɗaukar salo na ƙasa da ƙasa. Ya kuma bayyana irin yadda ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga Nijeriya...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu geopolitical bisa tsarin mulkin Amurka. A jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron tattaunawa na Tehran a jiya litinin, Qalibaf ya kara da cewa: A fagen siyasar kasa, siyasa ba ita ce kullin nauyi ba, a maimakon haka, labarin kasa shi ne ginshikin da siyasa ta ginu a kansa a matsayin wani mataki mai girma. Ya bayyana cewa: Idan ana magana game da ababen...
    Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke yammacin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, inda suka yi nasarar ritsawa da sojojin mamaya masu yawa da suka yi sanadaiyyar halakar wasu daga cikinsu bayan jikkata wasu da dama. Rundunar ta Al-Qassam ta ce: Mayakanta sun kai hari kan motocin sojin mamayar Isra’ila uku da bama-baman Shawaz guda biyu da kuma makami mai linzami, sannan kuma suka yi arangama da wata rundunar mamayar Isra’ila....
    Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka rattaba hannu tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979. Tashar talabijin ta NAN ta nakalto Eliyahu Dekel, tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma masani kan al’amuran Masar na cewa: Masar na cikin gaggawar shirin tunkarar rikicin soji, yana mai cewa “yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979 ta kasance cikin yanayi na rugujewa tun lokacin da...
    Ya ce, “Eh, an kama Galadi yau yayin da ake tantance shi da nufin zuwa Saudiyya.” Kama Galadi na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan kama wani riƙaƙƙen ɗan bindiga a sansanin alhazai da ke Abuja. Ana zargin mutumin da hannu a wasu manyan sace-sacen mutane a Jihar Kogi da Abuja. An shiga ruɗani yayin da wasu ke tambayar yadda mutanen da ake nema ke samun damar mallakar takardun tafiye-tafiye da wuce matakan tsaro ba tare da an gano su ba. Amma jami’in DSS ya ce wannan tambaya ta shafi sauran hukumomi da ke bayar da fasfo da kula da tafiye-tafiye. Ya ƙara da cewa, “Galadi yana hannunmu yanzu kuma yana amsa tambayoyi. Za a gurfanar da shi a kotu bayan...
    Ta kuma yi kira da a cafke masu safarar mutane tare da fallasa sunayensu bayan an gurfanar da su a gaban kotu, domin daƙile laifi. NiDCOM ta miƙa waɗanda aka ceto ga hukumar NAPTIP domin tantance su da kuma ci gaba da ba su kulawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwanan baya, yayin taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawar Sin da CELAC, shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya ziyarci kasar Sin, inda kuma ya zanta da kafar CMG a shirin “Hira da shugabanni”. Yayin tattaunawar, shugaba Petro ya ce ya sha ziyartar kasar Sin cikin shekaru 20 da suka gabata. Ya kuma yi imanin cewa, ayyukan kasar Sin sun nuna wani sabon salo na ci gaban zamantakewar al’ummar bil’adama. Ya ce kasar Sin ta samu gagarumar nasara a fannin raya tattalin arziki da kawar da talauci, daruruwan miliyoyin mutane sun tsira daga kangin talauci, kuma sha’anin kawar da talauci a duniya ya samu gagarumin ci gaba. Shugaba Petro ya kara da cewa, wadannan nasarori ba a iya raba...
    Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu 26. Wani mazaunin Ƙauran Namoda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce adadin mutanen zai iya cin haka, inda ya tabbatar cewa maharan sun kashe wata mata tare da sace wasu 26. Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wani magidanci da matansa biyu da ’ya’yansa uku. An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin...
    Da yammacin jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Luoyang na lardin Henan. A yayin ziyarar, Xi ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, da gidan ibada na “Farin Doki”, da kuma ramin dutse na Longmen. Ya fahimci yadda aka inganta ci gaban masana’antun samar da kayayyaki a wurin, da karfafa kiyayewa, da amfani da abubuwan tarihi da al’adu, da habaka ingantattun masana’antun al’adu da yawon shakatawa da sauransu. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    An dauke kashin farko na maniyyata 550 daga jihar jigawa zuwa Saudiyya a filin jirgin Nuhu Muhammadu Sunusi domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.   Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan tashinsu zuwa kasa mai tsarki.   Ya bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga kananan hukumomi 24 na jihar.   Ya ce kananan hukumomin sun hada da Kazaure, Roni, Gwiwa, Yankwashi, Gumel, Gagarawa, Garki, Maigatari, Suletankarkar, Babura, Jahun, da Miga.   Sauran sune Kafin Hausa, Auyo, Hadejia, Kirikasamma, Guri, Birniwa, Malam Madori, Dutse, Kiyawa, Ringim da Gwaram.   Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yi nuni da cewa jirgin ya kuma kunshi wasu jami’an hukumar alhazai ta jiha da na likitoci da...
    Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi na Sultan Abubakar da ke jihar. An kama shi ne a safiyar ranar Litinin, washegarin da jami’an tsaro suka kama wani ɗan bindiga yana yana shirin hawa mota zuwa filin jirgin sama na Abuja domin zuwa aikin Hajji. Ɗan bindigar da aka kama a Abuja, ya kasance jami’an tsaro na nemansa kan ayyukan garkuwa da mutane a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Kogi....
    Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi na Sultan Abubakar da ke jihar. An kama shi ne a safiyar ranar Litinin, washegarin da jami’an tsaro suka kama wani ɗan bindiga yana yana shirin hawa mota zuwa filin jirgin sama na Abuja domin zuwa aikin Hajji. Ɗan bindigar da aka kama a Abuja, ya kasance jami’an tsaro na nemansa kan ayyukan garkuwa da mutane a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Kogi....
    Wani jami’in hukumar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa tsare-tsaren da hukumar ta ɗauka sun taimaka sosai, inda komai ke tafiya cikin kwanciyar hankali a Saudiyya. An fara jigilar maniyyatan ne a ranar 9 ga watan Mayu 2025 a filin jirgin sama na Owerri da ke Jihar Imo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji. An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji. Ado Aliero shugaban ’yan bindiga ne da ya yi ƙaurin da yin garkuwa da mutane masu yawa a lokaci guda, musamman a Jihar Zamfara da maƙwabtanta. Kafar yada labarai ta ABN News ta bayyana cewa matan biyu sun canza sunayensu domin kada a gane su. An cimma matsaya kan dakatar da haska fina-finai 22 a Kano Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka. ” Zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne batutuwa mafi muhimmanci ga dukkan kasashen yankin,” in ji shi. Ya nanata matsayar Iran kan turbar diflomasiyya da kuma muhimmancin da take baiwa manufofin kyakkyawar makobtaka ta hanyar tattaunawa. A wani bangare na jawabin nasa, ministan harkokin wajen na Iran ya ce dandalin tattaunawa na Tehran karo na shida ya samu...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin na cewa tattaunawar ta yi amfani.” Rasha a shirye take ta yi aiki tare da Ukraine a kan wata yarjejeniya “game da samar da zaman lafiya a nan gaba.” “Rasha da Ukraine za su fara tattaunawa nan take domin tsagaita bude wuta,” in ji Trump. A cewar wata majiya kusa da tattaunawar da ke gudana, shugaban fadar White House ya tuntubi Volodymyr Zelensky “na ‘yan...