Leadership News Hausa:
2025-11-03@02:01:50 GMT

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

Published: 6th, July 2025 GMT

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

Sadau, ya ci gaba da bayyana yadda zai ci gaba rika tunawa da mahaifin nasu, inda ya ce; “Akwai abubuwa da dama da zan rika tuna mahaifina da su, amma abin da zan fi tunawa da shi, wanda kuma zan yi koyi da su shi ne kula da ibada, domin ba za a taba zuwa masallaci ka gan shi a sahu na biyu ba, koda-yaushe a sahun farko za ka gan shi.

In dai ibada ce, a gaba za ka gan shi; an shaide shi da haka”, in ji shi.

“Ina godiya ga yan Kannywood da sauran al’ummar da suka halarci jana’iza, wallahi har kwalla na yi saboda irin dandazon jama’a da na gani, Allah ya saka wa kowa da alhairi, sannan kuma ya ba mu hakurin rashin wannan mahaifi namu, muna fatan yadda ya samu kyakkyawar shaida a wajen mutane, ya sa ya samu wannan a can”.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka

Daga Yusuf Zubairu Kauru 

Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.

A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.

Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.

A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.

Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.

Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.

“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.

Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • Yadda Za Ku Hada Fab Biskit
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi