CORET Za Ta Samar da Ayyuka 3,000 Ga Matasa A Jihohin Kaduna Da Jigawa
Published: 17th, March 2025 GMT
Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika wato CORET, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, sun bayyana shirinsu na samar da ayyuka guda dubu uku ga matasa ta hanyar sarrafa madara a sarkar darajar madara a Jahohin Kaduna da Jigawa.
Shugaban Shirin na CORET, Dr.
Taron horaswar na tsawon kwanaki biyu ya haɗa shugabanni daga ƙungiyoyin kiwo na madara guda goma sha biyu, masu tara madara, da shugabannin al’umma. Wannan shiri da ECOWAS ta ɗauki nauyi, zai fara aiki gwaje ne a ƙauyuka biyu, a Ladduga a Jihar Kaduna da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.
Haka kuma, an samu goyon baya daga Hukumar Ci gaban Kasar Sweden, inda ake aiwatar da aikin ta hanyar haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi kamar Hukumar Kula da Makiyaya da kuma da sauran su.
Dr. Umar Hardo ya bayyana cewa taron horaswar na nufin bai wa ƙungiyoyin haɗin kai horo da ilimi a duk fannoni na samar da madara domin cigabansu
“CORET ta riga ta shiga haɗin gwiwa da kamfanoni irin su Milk Copal, Nestlé da Farm Fresh. Kuma an gina cibiyoyin tarin madara masu amfani da hasken rana a Ladduga da Maigatari,” in ji shi.
Dr. Umar Hardo ya ƙara da cewa an tsara horaswar ne akan matasa dari huɗu, amma matasa dari tara da ashirin da uku daga Ladduga suka nuna sha’awar shiga, lamarin da ya nuna yadda matasa ke da sha’awar shiga ƙungiyoyin haɗin gwiwa.
Ya ce daga cikinsu, an zaɓi matasa dari huɗu daga Maigatari, Jihar Jigawa don samun horo a cikin shirin.
“CORET ta sanya hannu kan yarjejeniya da Ma’aikatar Noma ta Tarayya da kuma Ma’aikatun Noma na Jihohin Kaduna da Jigawa domin aiwatar da wannan aiki,” in ji shi.
Shugaban Shirin ya bayyana cewa wannan wani babban cigaba ne a tarihin Najeriya, domin wannan ne karon farko da ake gina cibiyoyin tara madara masu na’urorin sanyaya madara domin sauƙin jigilar ta ba tare da ta lalace ba.
Ya ƙara da cewa wani sashi na shirin, shi ne gina cibiyoyin tara madara tare da horas da mahalarta a matsayin masu tara madara daga karkara waɗanda za su kula da wadannan cibiyoyi da kuma ƙungiyoyin haɗin ksn.
A cikin Kasidarshi, Tsohon Darakta na Raya Al’umma da Ƙungiyoyin Haɗin Kai a Jihar Kaduna, Mista Yohanna Kabirat, ya ce horon ya mayar da hankali ne kan ƙungiyoyin haɗin Kai da gudanarwa, da shugabanci domin su gudanar da ƙungiyoyinsu cikin nasara.
Ya jaddada muhimmancin ƙungiyoyin haɗin kai wajen ci gaba mai ɗorewa ga membobinsu, musamman matasa na Ladduga.
Mista Kabirat ya shawarci mahalarta su isar da ilimin da suka samu ga sauran membobinsu, musamman wajen yin bayanawa kowa bayyanai ba tareda an boye ba wanda shi ne babban kalubalen da ya jefa ƙungiyoyi da dama cikin matsalolin kudi a baya.
Tsohon Daraktan a karshe yace tushen nasarar kowace ƙungiyar haɗin Kai shine bin dokokin ƙungiyar yadda ya kamata.
Da suke magana da Radio Nigeria Kaduna, wasu daga cikin mahalarta taron, Sufyanu Umar da Fatima Isa, sun bayyana farin cikinsu da horon da aka basu, inda suka ce sun samu ƙwarewa ta musamman wajen tafiyar da ƙungiyoyinsu cikin nasara da inganci.
Mahalarta taron horaswar sun yaba wa CORET da sauran abokan ci gaba bisa shirya taron horaswar da suka ce zai sauya rayuwarsu ta fannin samar da madara.
Sun bayyana cewa ilimin da suka samu zai kasance ginshiƙi mai ɗorewa ga rayuwarsu da ci gabansu.
Rahoto daga Adamu Yusuf.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ayyuka Jigawa Samarda
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp