Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa
Published: 6th, July 2025 GMT
Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa karkashin tsarin hadakar BRICS, ya zamo wani muhimman karfi na ingiza nasarar samar da duniya mai mabanbantan tasiri, wadda za ta wanzu bisa daidaito da adalci, da kuma tsari mai game dukkanin sassa, da tattalin arziki da dukkanin duniya za ta ci gajiyarsa.
Kasashe mambobin BRICS, sun yi aiki tukuru wajen ingiza tsarin cinikayya da kudaden juna, da gina tsarin hada-hadar kudade mai zaman kansa, bisa shirye-shirye irin su sabon bankin samar da ci gaba, da tsarin yarjejeniyar adana kudade na ko ta kwana, da ingiza dabarun samar da ci gaba, da damammaki masu iya amfanar kasashe masu tasowa.
A kuri’un jin ra’ayin, kaso 94.7 bisa dari na masu bayyana mahangarsu na ganin tsarin hadin gwiwar BRICS, ba rage dogaron membobinta ya yi kan dalar Amurka kadai ba, har ma ya daukaka muryoyinsu cikin tsarin jagorancin hada-hadar kudade ta duniya. A daya bangaren kuma, kaso 89.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin yabawa tsarin suka yi, bisa yadda ya samar da dabarun kwaikwayo na zahiri, wadanda za su taimaka wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin duniya, da gina salon jagorancin duniya mai adalci da game dukkanin sassa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Yace Yana Jiran Amsar Hamas Cikin Sa’o’i 24 Masu Zuwa Don Tsagaita Wuta Na Kwanaki 60
Shugaban kasar Amurka Donal Trump Ya Bayyana cewa nan da kwana guda ko sa’o’ii 24 masu zuwa ne zai sani, ko kungiyar Hamas ta amince da ‘shawararsa ta tsagaita wuta da HKI kuma ta karshe a gaza.
Shafin yanar gizo ta labarai ‘Arabnews ta kasar Saudia’ ta nakalto Trump yana fadar haka a yau jumma’a.
A wani bangare shugaban ya ce yayi magana da gwamnatin kasar Saudia dangane da fadada yarjeniyar Ibrahimia wacce ya samar da ita a shugabancinsa na baya wacce take bukatar kasashen larabawa su samar da huldar jakadanci da HKI, wanda kuma ya sami nasarar a kan wasu kasashen larabawa na yankin tekun Farisa.
Daga shekara ta 2023 ya zuwa yanzu yahudawan sun kashe falasdinawa kimani 56,000 sannan fiye da dubu 12000 suka ji rauni.
Majiyar Falasdinawan ya zuwa yansu, ta bayyana cewa fatansu shi ne tsagait wutar ta kaika ta zamam din-din din.