Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [9]
Published: 17th, March 2025 GMT
Mataki na Uku: Kare kai daga shubuha; wato matakin tsantseni, shubuha na nufin abubuwan da ba a tabbatar da halacci ko haramcinsu ba. Akwai wani mataki da ya fi kauce wa haram, wato kauce wa abubuwan da ke da shakku. Annabi (SAW) ya ce:
” Lalle halal a bayyane take, kuma lalle haram a bayyane yake, amma akwai wasu abubuwa masu rikitarwa a tsakanin su waɗanda mutane da yawa ba su san su ba, wanda ya nisanci shubuha, to ya kare addininsa da mutuncinsa.
Mataki na Huɗu: Kare kai daga abubuwan da aka halatta; wato matakin gudun duniya. Wannan matakin ya fi zurfi domin yana nuni da zuhudu (wato yin watsi da son duniya). Duk da cewa akwai halal da aka ba wa mutum damar amfani da su, sai dai matakin mafi girman taƙawa shi ne rage kwaɗayin duniya domin kauce wa duk wani abu da zai shagaltar da mutum daga bautar Allah. Wannan ya dace da hadisin Annabi (SAW) da ya ce: “Ka kasance a duniya kamar baƙo, ko kuma kamar wani matafiyi.” Bukhari ne ya ruwaito. Don haka, matakin gudun duniya yana nuna cewa taƙawa ta gaskiya ba kawai da nisantar haram ba ce, har ma da rage dogaro da duniya don samun kyakkyawan sakamako a lahira.
Mataki na Biyar: Kare zuciya daga duk wani abu da ba Allah ba. Wato matakin bautar Allah kamar kana ganin Sa. Wannan shi ne matakin ihsani wanda Annabi (SAW) ya bayyana a hadisin Jibrilu da cewa:
“Ihsan shi ne ka bauta wa Allah kamar kana ganin Sa, idan ba ka ganin Sa, to Shi yana ganin ka.” Muslim ne ya ruwaito. Wannan matakin yana nuna tsarkake zuciya daga kowanne abu da zai shagaltar da mutum daga Allah. Ana son mai taƙawa ya kasance zuciyarsa a koyaushe a tare da Allah, yana ƙaunar Sa fiye da komai. Wannan matakin ne mafi girma a taƙawa, domin yana nuni da mutum ya kasance kullum yana jin tsoron Allah tare da ƙaunar Sa, ba wai kawai yana gudun azabarsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa.
Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa.
Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba.
NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaWannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan