Leadership News Hausa:
2025-07-05@18:37:51 GMT

ALGON Ta Taya Gwamnan Sani Murnar Samun Lambar Yabo Ta Kasa

Published: 5th, July 2025 GMT

ALGON Ta Taya Gwamnan Sani Murnar Samun Lambar Yabo Ta Kasa

Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai girma gwamna, da gagarumin nasarorin da ya samu a hukumance, da kuma jagoranci mai tsari da yake kai domin ci gaba da tsara tafiyar dimokuradiyyar kasa.

Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8) Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun sakataren yada labarai na ALGON, Muhammad Lawal Shehu a ranar Juma’a 4 ga watan Yulin 2025. Sanarwar ta kara da cewa, a lokacin da yake Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, ya taka muhimmiyar rawa inda ya dauki nauyin kudirori masu muhimmanci wadanda suka karfafa tsaron kasa, inganta yaki da cin hanci da rashawa, da kuma sabunta muhimman tsare-tsare na doka. Ta hanyar ba da fifikon ci gaban karkara, farfado da aikin noma, fadada hanyoyin samar da lafiya mai inganci, inganta rayuwar al’umma, da baiwa kananan hukumomi damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, Gwamna Uba Sani ya nuna jagoranci mai hangen nesa wanda ke daukaka rayuwar al’umma a fadin jihar Kaduna. ALGON reshen jihar Kaduna tana taya al’ummar jihar Kaduna da Nijeriya baki daya wajen murnar wannan gagarumin nasara da aka samu tare da addu’ar Allah ya kara basira da nasara a kan hidimar da yake yi wa jihar da kasa baki daya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: jihar Kaduna

এছাড়াও পড়ুন:

Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa

Ta la’akari da wannan yanayin da kasar Amurka ke ciki, ma iya cewa, ita kanta ta zama kamar wani dutse ne da ke fadowa, kuma tabbas wata rana zai taba kasa! (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8)
  • Kayayyakin Sin Na Kara Samun Karbuwa A Kasuwar Duniya
  • Ayyukan ‘Yan Ta’adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci
  • Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattaunawa Kan Zaman Lafiya Na Duniya Karo Na 13
  • Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa
  • Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro
  • Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
  • Buhari Ba Shi Da Lafiya, Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
  • Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi