Tsohuwar ɗaliba ta kai ƙarar makarantar da ta kammala
Published: 17th, March 2025 GMT
Wata matashiya mai suna Aleysha Ortiz ’yar shekara 19 da ke Jihar Connecticut a Amurka ta dauki matakin shari’a a kan tsohuwar makarantar sakandaren gwamnatin da ta yi saboda gazawarta ta hanyar ba ta damar kammala karatu “da sakamako mai daraja” duk da ta kasance maras ƙoƙari.
A watan Yunin shekarar bara ce, Aleysha Ortiz ta kammala karatu a Makarantar Hartford Public High School da ke Hartford, a Jihar Connecticut, inda aka karama ta, har ma ta samu gurbin karatu a kwaleji, amma yanzu ta kai karar tsohuwar makarantarta saboda sakacinta.
Matashiyar mai shekara 19 tana zargin makarantar da ta kammala da yin watsi da karatunta, tana mai cewa da ƙyar za ta iya riƙe fensir a hannunta kuma ƙoƙarin karatunta ya yi kama da na dalibi ɗan aji daya.
An haife ta a garin Puerto Rico, Aleysha tana fama da matsalolin koyo tun tana karama, kuma dabi’arta ta ci gaba bayan ta yi ƙaura zuwa Amurka tana ’yar shekara 5.
Ta yi iƙirarin cewa, makarantarta da kuma malaminta na musamman da aka ba ta ba su da wani amfani har sai wata guda kafin ta kammala karatunta a zango na ƙarshe lokacin da suka gudanar da ƙarin gwajin da take nema kuma suka gane cewa ba ta da ƙoƙari.
Jami’an hukumar makarantar sun shaida wa matashiyar cewa, za ta iya jinkirta karɓar takardar shaidar kammala karatunta na difiloma don sauya su da wasu ayyuka. Amma ta ƙi amincewa.
Ortiz ta bayyana wa CNN cewa, “Na yanke shawarar shigar da ƙara, yanzu lokacina ne,” inda ta ƙara da cewa, kammala karatunta da karramawa daga makarantar sakandare Hartford Public High School, wanda yawanci yana nufin ɗalibi ya nuna ƙwarewa a fannin ilimi.
Amma ta yaya Aleysha Ortiz za ta kammala karatun sakandare tare da karramawa yayin da ba ta iya karatu da rubutu ba? Ta yaya aka karɓe ta zuwa Jami’ar Connecticut?
Ta yi iƙirarin cewa, manhajojin zamani suna matuƙar taimakawa. Tana amfani da manhajojin wayar hannu don fassara rubutu zuwa murya da murya zuwa rubutu, har ma ta yi amfani da su wajen aikace-aikacen kwalejin da rubuce-rubucen da ake bukata. Kasancewarta ɗalibai kwalejin ya saka ta cikin yanayi na daban-daban.
Aleysha ta yarda cewa, inda ta daina zuwa ajin karatu a farkon Fabrairu. Ta so ta ɗauki lokaci don kula da lafiyar ƙwaƙwalwarta, amma tana fatan komawa azuzuwa nan ba da jimawa ba.
Aleysha ta ce, ta kai ƙarar tsohuwar makarantarta ce saboda tana son a tuhumi shugabanninta kan abin da ta fuskanta.
Ta yi ikirarin cewa, “ba su san abin da suke yi ba kuma ba su damu ba,” kuma tana fatan cewa, fafutukar da take yi a shari’ar zai hana wasu matasa rashin samun cikakken ilimi.
“Ni mutum ce mai matukar sha’awar karatu kuma ina son koyo,” in ji Ortiz.
“Mutane sun yi amfani da wannan damar don koyo, kuma yanzu ina kwaleji kuma ina so in yi amfani da wannan.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗaliba Makaranta kammala karatu
এছাড়াও পড়ুন:
Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu
Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya.
Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — DalungSanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya.
“Mu a matsayimmu na ƙasa mai son zaman lafiya, muna roƙon ƙasashen da ke rikici da su zauna su tattauna maimakon su ci gaba da faɗa.”
Gwamnatin Tarayya ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya, musamman Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da su ɗauki matakai don hana yaɗuwar rikicin da kuma samo hanyar warware matsalar.
Sanarwar ta ƙara da cewa amfani da ƙarfin soji ba shi da amfani matuƙa, domin faɗa ba zai kawo sauƙi ba.
Najeriya ta ce a shirye ta ke ta bayar da taimako domin hana yaɗuwar rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.