2027: Ana raɗe-raɗin Sanata Lamiɗo zai fice daga APC zuwa ADC
Published: 6th, July 2025 GMT
Jita-jita ta fara ƙarfi cewar Sanata Ibrahim Lamiɗo da ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, na shirin ficewa jam’iyyar APC zuwa ADC.
Wannan jita-jita ta fara ƙarfi ne bayan da wasu ‘yan siyasa suka haɗu don kafa sabuwar jam’iyya mai suna ADC da nufin kayar da APC a zaɓen 2027.
Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPPA cewar wasu, Sanata Lamiɗo ba ya mu’amala da gwamnatin APC a jihar inda alaƙarsa ta fi ƙarfi da ‘yan adawa.
Wannan ne ya sa ake ganin ba zai tsaya takara a APC ba a 2027.
Wani ɗan siyasa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Sanata Lamiɗo ba ya ga maciji da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Gwamna Ahmad Aliyu.
A cewarsa, “Sama da shekara ɗaya ba mu ga Sanata Lamiɗo a taron gwamnati ko na APC ba. Don haka ba za mu yi mamakin ficewarsa ba.”
Wani magoyin bayan APC, Kabiru Wurno, ya ce yana da tabbacin cewa Sanatan zai koma ADC.
“Lamiɗo yana son sake tsayawa takara a 2027, amma da wuya APC ta ba shi dama saboda ba ya tare da manyan jagororinta. Dole ya nemi wata hanya.”
Shu’aibu Muhammad daga Sabon Birni, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yiwuwar ficewar Sanatan.
“Da zai shirya da Wamakko, da za su yi ƙarfi tare. Siyasar Gabas tana buƙatar haɗin kai.”
Shi kuwa Ya’u Muhammad daga Goronyo ya ce, “Idan har Sanata Lamiɗo zai fice daga APC, muna tare da shi. Shi mutum ne da ke tallafa wa matasa da marasa galihu.”
Wani makusancin Sanatan ya ce ba zai ce uffan kan lamarin ba, zai bar Sanatan ya yi ƙarin haske.
Sai dai duk da ƙoƙarin jin ta bakin Sanata Lamiɗo haƙar Aminiya ba ta cimma ruwa ba.
Yanzu dai jama’a da dama na dakon jiran hukuncin da Sanatan zai ɗauka kafin babban taron jam’iyyar ADC da ke tafe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakkwato Takara Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.
Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata.
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.
Domin sauke shirin, latsa nan