Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu
Published: 5th, July 2025 GMT
A yau Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaran aikinsa na kasar Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 65, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
A cikin sakonsa Wang Yi ya bayyana cewa, cikin shekaru 65, an raya dangantaka tsakanin Sin da Ghana yadda ya kamata, kana an karfafa imani da juna kan harkokin siyasa, tare da samun manyan nasarori a hadin gwiwarsu ta fannoni daban daban.
Wang Yi ya ce, ana fatan yin kokari tare da minista Ablakwa, wajen kara fadada mu’ammala a tsakanin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu, da goyon bayan juna, da aiwatar da manufofi da aka amince da su, a gun taron koli na Beijing, na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, don sa kaimi ga daga dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Ghana zuwa sabon matsayi.
A nasa bangare, minista Ablakwa ya bayyana cewa, kasar Ghana na godewa Sin, bisa samar mata da gudummawa, da goyon baya a fannonin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Ya ce an samu manyan nasarori a fannin hadin gwiwar sassan biyu karkashin tsarin dandalin FOCAC, wanda hakan ya samar da babbar gudummawa ga kasashen Afirka ciki har da Ghana, wajen inganta karfinsu na samun ci gaba, kuma hakan zai amfani jama’ar kasashen Afirka baki daya. Bugu da kari, kasar Ghana tana fatan kokartawa tare da kasar Sin, wajen sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare yadda ya kamata. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato kudi fansa kimanin Naira miliyan 5 a yankunan Magumeri da Gajiram a jihar Borno.
Kakakin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanar Sani Uba , ya ce sojojin da suke sintiri a yankunan ne suka hallakan mayakan bayan sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan ta’addan a kusa da Goni Dunari a Karamar Hukumar Magumeri.
Sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025 ta ce, “Dakarun mu sun yi gaggawar daukar matakin dakile barazanar bayan da suka ga yadda ’yan ta’addan suka kona gidaje tare da tsoratar da mutanen yankin.”
Ya bayyana cewa sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan ne bayan sun shafe sa’o’i hudu suna bibiyar su, inda suka kashe mayaka biyar tare da tilasta wa sauran tserewa.
Soja ya harbe matarsa, ya kashe kansa a Jihar Neja Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoniKayayyakin da aka kwato sun haxa da bindiga kirar AK-47, alburusai, wuqa, da wayar hannu.
Uba ya qara da cewa “Babu asarar rayuka ko asarar kayan aiki da sojojin mu suka yi.”
A wani samamen kuma a hanyar Gajiram Bolori – Mile 40 – Gajiganna, sojoji sun yi arangama da mayakan Boko Haram a kusa da kauyen Zundur, inda suka kashe ’yan ta’adda hudu tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su daga Guzamala.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da wata mota, sabbin wayoyin hannu guda biyu, man fetur lita 30, da tsabar kudi da suka kai Naira miliyan 4.35.
Binciken farko ya nuna cewa ’yan ta’addan sun bukaci naira miliyan 2 da wayoyi biyu a matsayin kudin fansa ga dan uwan wadanda suka kama kafin sojojin su kai dauki.
Laftanar Kanar Uba ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka matsin lamba kan ’yan ta’addan tare da hana su sakat.