Aminiya:
2025-11-02@21:15:09 GMT

El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi

Published: 17th, March 2025 GMT

Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu.

Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu.

An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma

Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da gidauniyar ta fitar, wadda Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya sanya wa hannu.

A cewar takardar, dole ne El-Rufai ya fito ya yarda da laifinsa sannan ya nemi afuwar gidauniyar, ɗalibanta da jagoranta, Sheikh Ɗahiru Bauchi.

Gidauniyar ta zargi tsohon gwamnan da bayar da umarni ga jami’an tsaro don su kai samame a makarantun tsangayar Sheikh Ɗahiru Bauchi, inda aka kama wasu ɗaliban karatun Alƙur’ani har zuwa gidansa.

Har yanzu, akwai ɗaliban da ba a san inda suke ba.

Sayyadi ya bayyana cewa an yi hakan ne da gangan domin a tozarta Sheikh Ɗahiru Bauchi da kuma hana ci gaban ilimin addini da ya ke yi.

Ya ce idan har El-Rufai bai nemi afuwa ba kafin ƙarshen Ramadan, za su kai ƙararsa ga Shugaban Ƙasa, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, da kotu.

Idan kuwa duka ba su yi musu adalci ba, za su mika ƙarar ga Allah ta hanyar addu’a.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gidauniya Neman Afuwa Sheikh Ɗahiru Bauchi Sheikh Ɗahiru Bauchi

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya.

Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP

A lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu.

Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama sun ƙaryata jita-jitar.

A ranar Juma’a, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.

Ya yi iƙirarin cewar masu tsattsauran ra’ayi suna yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya .

Ya umarci ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar, Tom Cole, su binciki lamarin, sannan su gabatar masa da rahoto.

Shugaban ya ƙara da cewa ƙasarsa ba za ta zuba ido yayin da irin wannan “ta’addanci” ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe ba.

Ya lashi takobin cewar Amurka za ta ci gaba da kare Kiristoci a duniya baki ɗaya.

Bayan wannan furuci, wasu sun zargi Trump da amfani da matsalar tsaron Najeriya don samun goyon bayan siyasa.

Har yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta yi martani a kan lamarin ba, amma jami’an gwamnati a baya sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar suna da nasaba da ayyukan ta’addanci, fashi, da rikicin ƙabilanci, ba addini ba.

Kalmar “Ƙasa Mai Matsala Ta Musamman” na nufin ƙasashen da Amurka ke ganin suna take haƙƙin ’yancin addini, kuma hakan na iya sa wa ta ƙaƙaba wa Najeriya takunkumai.

Idan ba a manta Najeriya ta fara shiga jerin irin waɗanda ƙasashe tun a shekarar 2020.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure