EFCC ta kama Murja Kunya kan wulaƙanta takardun Naira
Published: 17th, March 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira.
NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru BauchiWata majiya daga EFCC ta tabbatar da cewa an kama Murja a ranar Asabar a Kano, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin, a cewar Gidan Rediyon Freedom da ke Kano.
Majiyar hukumar ta ce idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da ake zarginta da aikatawa.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Murja kimanin makonni uku da suka gabata, amma ta tsere daga beli kafin sake kama ta a ranar Asabar ɗin.
Murja Kunya ta yi kaurin suna tun bayan fara amfani da kafafen sada zumunta a matsayin abin barkwanci, kafin daga bisani ta mayar da shi dandalin sana’a.
A tsawon lokaci, ta shahara musamman a TikTok, inda take amfani da sunan “Yagayagamen,” duk da cewa a bayan nan ta jawo ce-ce-ku-ce a kanta.
A bayan nan dai hukumar ta EFCC ta cafke wasu abokan sana’ar Murja ’yan TikTok irinsu Alamin G-Fresh da Ashir Idris kan makamancin wannan zargi na wulaƙanta takardun kuɗi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano Murja Ibrahim Kunya
এছাড়াও পড়ুন:
Liverpool Sun Zama Zakaran Gasar Premier Bayan Lallasa Tottenham
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp