Leadership News Hausa:
2025-07-05@18:35:55 GMT

Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

Published: 5th, July 2025 GMT

Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

Yadda za’a hada:

Asamu biredi mai yanka-yanka a shafe shi da bota a ajiye a gefe.

Sai a zuba mai a cikin karamin kaskon miya sai a zuba yankakkiyar albasa a dan soya na minti biyu, sai a zuba jajjagagen su attaruhu din nan a ci gaba da soyawa. A zuba kayan kamshi da kayan dandano, sai a zuba yankakken kabeji.

Idan aka tabbatar duk sun soyu sai a dauki kifin gwangwani a tsiyaye man cikinsa sai a faffasa shi a zuba a kai a ci gaba da juyawa har komai ya hade jikinsa.

Akunna injin gasa buredi, sai a dauko wannan buredi mai yanka-yanka wanda aka shafa bota a jiki sai a zuba wannan hadin su kifin nan a jikin bari daya na biredin a tabbatar ko ina ya samu sai dauko wani biredin a rufe da shi.

Sai a dinga jera wannan biredin a cikin injin gashin a rufeta. Idan ya gasu za’ a ji yana kamshi, sai a bude a cire. Ana sha da shayi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Maduro Ya Jinjina Wa Jagororin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu
  • Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8)
  • Ku Zama Cikin Shirin Samun Sauyin Yanayi – NiMet
  • Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar
  • Haɗarin Da Ke Ƙunshe Da Jin Ɓangare Ɗaya Na Labari
  • Sin Na Fatan Yin Tafiya Bai Daya Tare Da Amurka 
  • Kuriar Jin Raayoyin Jamaa Na CGTN Ta Shaida Yadda Akasarin Jamaa Ke Ganin Baiken Kudurin Dokar Bunkasa Amurka
  • Zamfara Babban Wuri Ne Na Aikin Noma Mai Amfani Da Hasken Rana – Gwamna Lawal