Yadiot Ahranot: Amurka Ta Bayyana Lokacin Ficewarta Daga Syria
Published: 16th, April 2025 GMT
Jaridar “Yadiot-Ahranot” ta rubuta cewa, jami’an Amurka sun sanar da sojojin Isra’ila a lokacin da za ta janye sojojinta daga kasar Syria.
Jaridar ta ce, jami’an tsaron kasar ta Amurka sun fada wa sojojin Isra’ila cewa, janye sojojin nata zai fara ne nan da watanni biyu masu zuwa.
Rahoton jaridar ta ‘yan sahayoniya ya ce, Shirin janyewar sojojin na Amurka bai zama abin mamaki ba,domin tun farkon rantsar da Donald Trump ne ya bayyana aniyarsa na janye sojojin kasar daga Syria.
HKI tana jin cewa, idan har Amurkan ta janye daga kasar Syria, to Turkiya za ta kara azamarta ta shimfida ikonta a cikin kasar.
Tun a Zangon shugabancinsa na farko ne dai Donald Trump ya bayyana cewa Idan kungiyar “Da’esh” ta kare,to kuwa kasarsa za ta janye sojojinta daga Syria.Daga baya kuma ya sanar da cewa janyewar sojojin za ta kasance ne sannu a hankali.
Ita kuwa ma’aikatar tsaron kasar ta Amurka ta sanar da cewa; An riga an rattaba hannu akan batun janyewar sojojin daga Syria.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba October 30, 2025
Daga Birnin Sin Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21 October 30, 2025
Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025