Sudan Ta Kai Karar HDL A Gaban Kotun Kasa Da Kasa Ta MDD
Published: 11th, April 2025 GMT
Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa.
A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL da ta kawo karshen kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Masalit da sauran al’ummu a cikin tsawon shekaru biyu na yakin basasar kasar.
Ministan shari’a na kasar Sudan Muawia Usman ya bayyana cewa: Kisan kiyashin da dakarun kai daukin gaggawa su ka yi wa al’ummar Masalit da su ka kunshi larabawan yankin Darfur, ya faru ne ta hanyar taimakon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.”
Bayan da ministan na Sudan ya gama shigar da kara, gwamnatin HDL ta bayyana cewa, koken da Sudan din ta yi a kanta bai cika ka’idoji ba, kuma babu dalilai da za su tabbatar da abinda take fada.
Dukkanin kasashen biyu na Sudan da HDL suna cikin wadanda suka rattaba hannu akan yarjejeniyar 1948 wacce ta haramta kisan kiyashi, sai dai kuma kasar ta HDL ta nuna dari-dari akan wasu daga cikin bangarorin yarjejeniyar.
Kotun ta bayyana cewa; dari-darin da kasar ta HDI ta nuna akan wani sashe na yarjejeniyar zai iya hana ci gaba da gudanar da shari’ar.
Tun a cikin watan Aprilu na 2023 ne kasar ta Sudan ta fada cikin yakin basaasa.MDD ta ce fiye da mutane 24,000 ne su ka kwanta daya, yayin da wasu miliyan 14 su ka zama ‘yan gudun hijira, da hakan yake a matsayin kaso 30% na jumillar mutanen kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA