Gwamnati ta gargaɗi jihohi 30 kan ambaliyar ruwa
Published: 11th, April 2025 GMT
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Riɓers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a ranar Alhamis, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a gaɓar teku da koguna a wasu sassan yankunan Kudu maso Kudu na ƙasar, sakamakon ƙaruwar ruwan teku.
Daga cikin waɗannan jahohin akwai: Bayelsa, Cross Riɓer, Delta, da Ribas yayin da Akwa-Ibom da Edo suka faza cikin jihohin da ake fargabar yin ambaliyar.
Utseɓ ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da taron shekara na 2025 (AFO) na hasashen ambaliyar ruwa da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) ta gudanar a Abuja.
A taron na 2025 na Shekara-shekara kan Ambaliyar Ruwa (AFO) an raba su zuwa sassa uku don magance ƙalubalen iftila’in ambaliya da ba da bayanai don rage faruwar hakan, musamman a cikin unguwannin jama’a masu rauni.
Ministan ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta kasance ɗaya daga cikin ibtila’o’in da suka fi yin ɓarna a Nijeriya tare da sauyin yanayi da ke ƙara ƙaimi da tsanani.
Ya bayyana cewa unguwanni 1,249 a ƙananan hukumomi 176 a faɗin jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja sun faɗa cikin yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa a wannan shekarar, yayin da ƙarin unguwanni 2,187 a ƙananan hukumomi 293 ke fuskantar haɗarin ambaliya. Muhimman wuraren da ke da haɗarin sun haɗa da Abia, Benue, Lagos, Bayelsa, Riɓers, Jigawa, da dai sauransu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamawa Akwa Ibom Anambra Bayelsa Jigawa Kwara Nasarawa Taraba Zamfara ambaliyar ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina
Fitaccen attajirin nan Alhaji Dahiru Mangal, ya ɗauki nauyin yi wa marasa galihu a Jihar Katsina aikin ido kyauta, inda ɗaruruwan mutane ke samun kulawar likitoci ba tare da biyan ko sisi ba.
A yayin da wakilin Aminiya, ya ziyarci Asibitin Ido da ke birnin Katsina, marasa lafiya da dama da suka ci gajiyar aikin sun bayyana farin cikinsu da godiya kan tallafin na sama da Naira miliyan 257.
Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699 Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam SandaMalama Indo, wadda ta fito daga garin Dankama da ke Ƙaramar Hukumar Kaita, ta bayyana farin cikinta da samun tallafin.
Ta ce: “Na kwashe kusan shekara guda ina fama da ciwon ido. Da zarar yamma ta fara yi, sai na kasa fitowa saboda duhu. Amma yanzu ina gani lafiya lau, babu wata matsala.
“Mun kwana uku a nan asibiti, ba mu rasa komai ba, har abinci ake ba mu. Wallahi ba zan iya cewa na kashe komai ba sai kuɗin mota kawai.
“Muna roƙon Allah Ya saka wa wanda ya ɗauki nauyin wannan aiki da alheri,” in ji ta.
Shi ma wani dattijo mai suna Malam Khalha Jibiya, ya bayyana jin daɗinsa game da aikin.
Ya ce an masa aiki, an kuma ba shi tabarau, sannan yanzu yana gani ba tare da wata matsala ba.
“Idan waɗanda Allah Ya hore musu dukiya za su riƙa taimaka wa gajiyayyu kamar haka, da matsalolinmu da dama sun ragu.
“Muna addu’a Allah Ya saka wa mai ɗaukar nauyin wannan shiri da alheri.” inji Malam Khalha.
Dukkanin marasa lafiyan da Aminiya ta zanta da su, sun yi godiya, musamman ganin cewa aikin ido da magungunan da ake ba su kyauta ne baki ɗaya.