Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
Published: 18th, April 2025 GMT
A cikin dan kankanin lokacin da wannan hukuma ta fara aiki, ta horar da matasa sama da 100,000 horo kan shirye-shiryen koyon sana’o’i daban-daban a fannonin noma, ICT, kananan sana’o’i da dai sauran su, gwamnatin jihar ta bayar da tallafi da jarin sama da Naira biliyan 1.7 ga wadannan matasa domin fara sana’o’i.
Jihar jigawa jiha ce mai girma ta kuma yi fice a fannin noma a kokarin gwamnati na inganta rayuwar al’umma ta hanyar sabbin manufofin noma da ya zama abin a yaba.
Domin tabbatar da samar da wadataccen kayan aikin noma akai-akai, gwamnatin jihar ta zuba Naira biliyan 5 ga kamfanin samar da aikin gona na Jihar Jigawa (JASCO).
Haka zalika, Gwamnatin Namadi ta samar da sabbin tsare-tsare a fannin noma ta hanyar inganta tsarin samar da shinkafa, alkama, sesame da hibiscus domin bunkasa yankunan jihar.
A tsawon lokacin da ake bitar, jihar ta sayi tan 9,200 na taki, tarakta 60, tare da motocin girbi 10 gami da samar da fili mai fadin hekta 40,000 don shirin noman alkama wanda ya zama hadin gwiwa ne da gwamnatin tarayya.
Gwamnatin jihar ta kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna MOU da Bankin Duniya, Bankin Raya Afirka da Bankin Raya Musulunci a fannin noma da dai sauransu.
Haka kuma ayyukan da gwamnatin Namadi ta yi a fannin ilimi ba boyayye ba ne.
Shi ne Gwamna daya tilo a Nijeriya da ya zarce shawarar da UNESCO ta bayar na samar da kaso 25 a kasafin kudi ta fannin ilimi, wanda wannan shi ne karon farko da aka samu a tarinhin Jihar Jigawa da watakila a Arewacin Nijeriya.
Sannan Gwamna Namadi ya ware kashi 32 na kasafin kudi wa fannin ilimi, wanda ba kasafai ake samu ba a Nijeriya. Ya kara wa dalibai tallafin karatu da kashi 100 yayin da ya kara kudin ciyar da dalibai da kashi 40 cikin 100.
Har ila yau, gwamnatinsa ta dauki dalibai 150 da suka kammala karatun digiri na farko a jihar a matsayin malamai a manyan makarantun jihar yayin da aka bai wa malamai 3,570 aikin yi a makarantun firamare da sakandare a fadin jihar ta hanyar shirin J-Teach. haka kuma gwamnati ta gina manyan makarantun sakandare a jihar .
Domin magance matsalar yara da ba sa zuwa makaranta, gwamnatin ta bullo da sabbin makarantu na Mega Tsangaya tare da cibiyoyin ilimi da fasaha na yammacin Turai don magance wannan matsalar.
Jihar ta kuma hada gwiwa da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Nijeriya NITDA, domin horo gami da zurfafa ilimin malaman Jigawa da basu kwarewa ta fasahar sadarwa ICT saboda bunkasa fasaharsu ta koyarwa.
Bugu da kari, a fannin lafiya an samu sauye-sauye da dama a wannan bangare da ya shafi ma’aikatan lafiya a jihar inda aka fitar da Naira biliyan 17.2 domin kammala ayyukan asibitoci daban-daban a fadin jihar.
Gwamnatin ta kuma fitar da asusun kula da lafiya na Naira biliyan 1.2 domin kafa tsarin kiwon lafiya na Inshora ga gidaje sama da 140,000 tare da mutane 500 da suka cancanta a dukkan gundumomi 287 da ke fadin jihar.
Gwamnatin jihar ta shirya gina Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko a kowace Unguwa da kuma Babban Asibiti daya a kowace mazaba.
Gwamna Namadi ya kuma jajirce wajen tunkarar kalubalen da talakawa da marasa galihu ke fuskanta a cikin al’umma. Ya sanya an gudanar da kidayar gidajen marayu, nakasassu, tsofaffi da sauran su domin taimaka musu, sannan ya kara alawus din Tsaron Jama’a daga Naira 7000 zuwa 10,000.
Wani bangare na rangadin da Gwamnan ya fara a duk fadin yankin mazabu shi ne, jin ta bakin talakawa kai tsaye domin samar da mafita mai dorewa ga marasa galihu a cikin al’ummarmu.
Haka kuma gwamna ya sake samar da wasu tsare-tsare a fannin lafiya domin saukaka wa majinyata masu fama da cutuka masu tsanani kamar su ciwon koda, ciwon daji da kuma hanta a jihar ta hanyar biyan kudaden majinyatan da suka jima da larurar domin ganin sun warke daga cutar.
A kasa da shekaru biyu, Gwamna Namadi ya nuna kwarewa, iya aiki da kuma jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummar jihar kuma sakamakon hakan ne yake ta samun lambobin yabo na karramawa a fadin kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gwamna Namadi Jigawa Gwamnatin jihar ta gwamnatin jihar ta Naira biliyan Jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta fara yi wa maniyyata rigakafin cututtuka kafin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rigakafin da aka gudanar a harabar hukumar da ke Ilori, shugaban hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya bayyana rigakafin a matsayin wani sharadi da ya zamto wajibi ga dukkan Alhazai bisa umarnin gwamnatin Saudiyya.
Ya ce yin rigakafin yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar Alhazai a lokacin gudanar da aikin Hajji.
A cewarsa, an shirya shirin rigakafin ne domin hana yaduwar cututtuka da kuma tabbatar da cewa Alhazai sun samu lafiya da kwanciyar hankali yayin aikin Hajjin.
Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara jigilar rukuni na farko na Alhazai daga jihar zuwa ƙasar Saudiyya ranar 12 ga watan Mayu.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa za a kammala aikin rigakafin ne ranar Laraba 30 ga watan Mayu, sannan kuma za a fara raba tufafi da jakunkunan tafiya nan take.
Alhaji Abdulkadir ya yi kira ga maniyyatan da su kammala duk shirye-shiryen lafiyar jiki da na tafiya cikin lokacin da aka kayyade domin samun nasarar aikin Hajjin ba tare da wata tangarda ba.
Ali Muhammad Rabi’u