Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
Published: 18th, April 2025 GMT
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara, ta tura jami’ai 415 a fadin jihar domin tabbatar da tsaro a duk lokacin bukukuwan Easter.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar, ASCII Umar Mohammad M. ya fitar, ya ce jami’an sun jibge a wuraren ibada daban-daban da sauran muhimman wurare a fadin kananan hukumomi 14 na jihar domin tabbatar da tsaro da kuma gudanar da bukukuwan lafiya.
A cewar sanarwar, kwamandan jihar, Sani Mustapha, ya jaddada kudirin hukumar NSCDC karkashin jagorancin kwamandan Janar, Dakta Ahmed Abubakar Audi, na magance matsalolin tsaro a fadin kasar nan.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar a jihar Zamfara ta shirya tsaf domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata tare da bayar da gudumawa wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.
REL/AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a cikin jihar da ƴan ta’adda ko ƴan bindiga ke da iko da ita. Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a ranar Talata.
Gwamna Mutfwang ya ce gwamnatinsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro, musamman ta hanyar farfaɗo da rundunar tsaron cikin gida ta jihar wato Operation Rainbow, domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ana Ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Malam Adamu Fika Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A FilatoYa ƙara da cewa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an dawo da zaman lafiya a sassan jihar da rikice-rikicen ƙabilanci ko na addini suka taɓa. Ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya domin tabbatar da fahimtar juna da daidaiton al’umma.
Gwamnan ya sake jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya. Ya ce kafa ƴansandan jiha zai bai wa gwamnatocin jihohi damar yin tsari da ɗaukar matakan da suka dace da yanayin tsaron yankunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp