Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Shirya Taron Bita Ga Mahajjata a Jihar Kwara
Published: 16th, April 2025 GMT
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta kammala shirye-shirye domin fara taron bita ga maniyyata aikin Hajjin bana.
Shugaban Hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilori.
Ya shawarci dukkan maniyyata da su halarci wannan muhimmin shiri, yana mai cewa za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda ake gudanar da ibadar Hajji.
Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara gudanar da taron bitar ne a harabar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar daga ranar Lahadi, 20 ga watan Afirilun 2025.
Shugaban ya ƙara da cewa babban limamin masallacin Juma’a na Ilori, Sheikh Imam Mohammed Bashir, tare da wasu malaman addini daga sassa daban-daban na jihar za su jagoranci addu’a ta musamman domin samun tsaro da nasara ga maniyyatan.
Ali Muhammad Rabi’u
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jihar Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Dandalin SCO Na 2025
A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa, rage talauci wanda batu ne da ya shafi duniya baki daya, buri ne na daukacin kasashen duniya. Ya ce duk da cewa aiki ne mai matukar wahala, amma duk da haka kasar Sin ta cimma nasarar rage shi daidai da ajandar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030, shekaru 10 gabanin wa’adin karshe na ajandar.
Hakan ya shaida ingancin turba mai halayyar musamman da kasar Sin ke bi wajen rage talauci, tare da rubuta wani sabon babi a tarihin bil’adama ta fuskar yaki da fatara. Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada cewa, karancin ci gaba shi ne tushen talauci, kuma dandalin SCO ya aiwatar da managartan matakai a fannin rage talauci, da wanzar da ci gaba a shekarun baya bayan nan, kuma hakan ya haifar da tarin sakamako masu gamsarwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp